Fitsararriyar mawakiya Nicky Minaj za ta amarce nan da kwanaki bakwai

Fitsararriyar mawakiya Nicky Minaj za ta amarce nan da kwanaki bakwai

- Fitsararriyar mawakiya Nicky Minaj ta bayyana ranar da za ta amarce

- Mawakiya ta ce yanzu haka babu wani abu mafi muhimmanci a gabanta kamar tayi aure ta tara iyali

- Ta ce daga nan zuwa mako mai zuwa ana iya daura mata aure da saurayinta Kenneth

Fitsararriyar mawakiyar nan 'yar kasar Amurka Nicky Minaj ta bayyana cewa akwai yiwuwar za sy yi aure da saurayinta Kenneth Petty nan da kwanaki bakwai.

Mawakiyar mai shekaru 36, wacce take soyayya da masoyinta Kenneth Petty mai shekaru 41, ta bayyanawa manema labarai cewa suna iya yin auren nan da mako daya mai zuwa.

"Mun riga mun karbi lasisin mu na yin aure, amma akwai wata Fasto guda daya da nake so ta daura mana aure, na samu munyi magana da ita yau."

Ta bayyana mini cewa babu abinda za ta yi a cikin makon nan, hakan yasa zamu yi amfani da wannan damar ta daura mana aure cikin wannan makon.

Da aka tambayeta shin ta zabi kayan da za ta saka ranar daurin aure, sai ta ce: "Idan na ce sai na nemo kayan da zan saka ranar daurin aure abin zai dauki lokaci sosai, ni ban san yadda ake zabar kayan biki ba, amma zamu yi nan da shekara daya ko biyu."

KU KARANTA: Bidiyo: Ta tabbata ya koma fim, an nuno sabon fim din da Sanata Dino Melaye ya fito a ciki

Ta kara da cewa ita da saurayin nata suna son junan su, ta ce yanzu yin aure da tara iyali shine abu mafi muhimmanci da ta sanya a gaba.

"Mun shaku sosai da shi, saboda mun taso tun muna yara tare, kuma muna son junan mu."

Sai dai kuma masoyan mawakiyar suna ganin kamar cewa mawakiyar tayi gaggawa idan tayi aure yanzu, inda ita kuma ta kawo karshen kace nace bayan ta ce: "Mutane na iya fadar duk abinda suka ga dama, mutum daya ne zai iya fada mini abinda zan yi a rayuwa, shine masoyina, amma idan ba shi ba babu wani mutum a duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel