Masu aikin Umrah 35 sun kone kurmus har lahira a birnin Makkah

Masu aikin Umrah 35 sun kone kurmus har lahira a birnin Makkah

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun kawo cewa mutane 35 dake aikin umurah sun mutu sakamakon hatsarin motar da yayi sanadiyar konewarsu kurmus har lahira.

Wadanda lamarin ya shafa da suka kasance baki daga kasashen waje, sun kone kurmus har lahira a mummunan hatsarin da ya faru a hayar Hijrah kusa da Madina a yammacin ranar Laraba.

Bas din ta yi taho-mu-gama ne da wata motar daukar kaya a al-Akhal da misalin karfe 7:00 na yamma agogon kasar a ranar Laraba, karfe 5:00 kenan agogon Najeriya.

Zuwa yanzu ba a iya tabbatar da kasashen da suka fito ba, sai dai Firaministan kasar Indiya ya ce "ya kadu" da jin labarin hatsarin.

An kwashi mutane hudu da suka ji rauni mai tsanani zuwa asibiti, wata jaridar Saudiyya, Saudi Gazette ta ruwaito.

Jaridar ta bayyana cewa sarkin Madina Yarima Faisal Bin Salman ya bada umurnin a ba wadanda suka jikkata cikakken kulawa.

A cewar rahoton, mutane 34 ne suka rasa rayukansu nan take, sannan wani ya mutu a asibiti sanadiyyar raunin da ya ji.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Rundunar yan sanda ta shirya tura jami’ai sama da 30,000

Kakakin rundunan yan sandan Madina yace hukumomin sun kaddamar da bincike kan lamarin; inda ya bayyana cewa hukumomin tsaro da jami’an agaji na Saudiyya sun isa inda hatsarin ya faru cikin gaggawa bayan samun labarin hatsarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel