Najeriya za ta ba ainihin masu kamfanin wutan lantarkin YEDC kudinsu

Najeriya za ta ba ainihin masu kamfanin wutan lantarkin YEDC kudinsu

Rahotanni na zuwa mana cewa ana shirin maidawa asalin kamfanin da ke da alhakin rabawa jama’an Yola da kewaye wutan lantarki kudinta domin a karkare wani tsohon ciniki.

Gwamnatin Najeriya za ta maidawa kamfanin nan Yola Electricity Distribution Company wanda ake kira YEDC kudin da su ka sa na Naira biliyan 26.9 bayan an saida kamfanin wutan kasar.

Kamar yadda rahotanni su ka nuna gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta maidawa kamfanin wutan kudinsu ne a shekara mai zuwa na 2020 inda ta ware tarin kudi domin hakan.

A cikin kasafin kudin da shugaban kasa Buhari ya gabatar a majalisa, gwamnati ta fitar da Naira biliyan 10.9 daga cikin biliyan 26.9 da za a ba masu kamfanin na YEDC masu raba wuta a kasar.

KU KARANTA: Wasu kamfanonin lantarki sun tara makukun bashi a kan wuyansu

Kamfanin lantarkin nan YEDC ya na cikin manyan kamfanoni 11 da aka saidawa lantarkin Najeriya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan inda aka ba su alhakin kai wa jama’a wuta.

Integrated Energy Distribution and Marketing Company ne su ka saye 60% na YEDC bayan sun biya Dala miliyan 146.8 a shekarar 2013. A 2015 wannan yarjejeniya da aka yi ta tashi.

Kwanakin baya Yola Disco sun yi yunkurin sayen kamfanin a kan Naira biliyan 17.67, bayan an ce masu albarka ne su ka kara kudin zuwa Naira biliyan 19. A haka aka kuma amince.

Cinikin da ake ta faman yi ne ya yi tsawo har yanzu ba a kai ga sallamar masu kamfanin ba. Ana dai sa ran cewa a badi, a karkare wannan magana da zarar kwamitin NCP ta sa hannu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel