Tirkashi: Daliba ta bayyana yadda hirarsu da wani Lakcara ta kaya wanda ya nemi yayi zina da ita

Tirkashi: Daliba ta bayyana yadda hirarsu da wani Lakcara ta kaya wanda ya nemi yayi zina da ita

- Wata budurwa ta wallafa wata hira da suka yi da wani malamin jami'ar da take

- Budurwar ta wallafa hirar ne bayan ya kayar da ita jarrabawa saboda taki yadda ta kwanta da shi

- Haka kuma budurwar ta wallafa hadda hotunan irin hirar da suka yi da malamin na ta

Bayan bayyanar tonon sililin da ake yiwa malaman jami'a akan lalata da suke yi da dalibai su ba su maki, wata budurwa mai suna Busayo ta bayyana yadda tayi fama da wani dan iskan malamin jami'a.

A cewar ta Lakcaran wanda ta bayyana sunansa da Dr. Abdul ya fadar da ita jarrabawar shi saboda ta ki yarda ta yi lalata da shi.

Budurwar ta kuma wallafa hotunan hirar da suka yi da shi a manhajar WhatsApp domin tabbatar da faruwar lamarin.

KU KARANTA: An binciko yawan kudin da barayin Najeriya suka sata tun daga lokacin samun 'yancin kai zuwa yanzu

A hotunan da ta wallafa na hirar ta su a WhatsApp din, malamin yana ta faman rokon ta gafara amma ita kuma ta yi kunnen uwar shegu da shi.

A hirar ta su Busayo ta yi ta zagin Lakcaran, hakan na nuni da cewa har yanzu ta na jin haushin irin abinda Dr. Abdul ya yi mata.

Ga dai hotunan da Busayo ta wallafa na hirar da suka yi da Malamin Jami'ar a kasa:

Tirkashi: Daliba ta bayyana yadda hirarsu da wani Lakcara ta kaya wanda ya nemi yayi zina da ita
Busayo
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel