Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da sauransu su 45 a Kaduna

Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da sauransu su 45 a Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kama masu garkuwa da mutane da yan fashi da makami su 45, wadanda suka addabi matafiya da mazauna jihar a hanyar babbar titin Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Daga cikin masu laifin akwai wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Ahmadu Bello, Zaria su uku da kuma dan majalisar dokokin jihar Kaduna Suleiman Sabo.

Da yake jawabi ya manema labarai, kwamishinan yan sandan jihar, Ali Janga, ya bayyana cewa an kama su ne a wurare daban-daban a lokacin ayyuka da dama da jami’an rundunar suka gudanar.

A cewarsa, masu laifin sun karbi bakin kashe jami’an tawagar shugaban yan sanda na IRT guda uku a shekarar 2018 da kuma garkuwa da akayi da babban malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Algarkawi da aka yi kwanan nan da dai sauran laifuffuka.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Masu garkuwa da mutane sun sace jami’in tsaro, matarsa da dansa a birnin tarayya

A wani lamarin kuma, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Niger, inda suka fatattaki mutane sama da 1200 daga gidajensu a yankin.

Sabbin hare-haren da aka kai kan garuruwan Gyaramiya, Bataron Jatau da Bataron Waziri ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel