Dan sanda abokin kowa: Dan sanda ya yiwa wani mai mota dukan tsiya, saboda kawai yazo ya wuce shi a mota

Dan sanda abokin kowa: Dan sanda ya yiwa wani mai mota dukan tsiya, saboda kawai yazo ya wuce shi a mota

- Wani dan sanda ya yiwa wani mutumi dukan tsiya saboda yayi masa ham kuma ya zo ya wuce shi a mota

- Dan sandan dai an bayyana cewa Insfecta ne da yake aiki a helkwatar 'yan sanda ta Calabar

- An bayyana cewa bayan duka har bindiga ya fito da ita ya dinga harbawa wajen da mutumin yake

Ana zargin wani jami'in dan sanda da yiwa wani mutumi mutumi dukan tsiya sannan ya bi shi da harbi akan babbar hanya, saboda yayi kokarin wuce shi da mota.

An bayyana cewa wannan lamari ya faru a ranar Asabar dinnan da ta gabata da yamma, a garin Calabar dake jihar Cross River.

A yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Adekunle Adewumi, wanda yake aiki da wani kamfanin hada magunguna dake jihar Legas, dan sandan ya tunzura a lokacin da ya danna ham din motar shi a lokacin da yake kokarin wuce shi.

An bayyana sunan dan sandan da yayi wannan aika-aika da Andy Amama, wanda yake Inspector ne da yake aiki a helkwatar 'yan sanda dake Calabar.

Mutumin yace yayi kokarin wuce dan sandan ne saboda yaga yana yin tukin da bai kamata, yana yawo akan titi daga nan ya dawo nan.

"Ya sani dole nayi kokarin wuce shi, saboda gujewa hadari. Amma duk da haka ya zo ta kusa dani ya daki kofar motata ta baya."

Ya ce lokacin da ya fito daga motar domin duba irin barnar da yayi masa, dan sandan sai ya zo ya naushe shi a fuska, ya ture shi ya fadi kasa, sannan ya dinga dukan shi.

"A lokacin da yake duka na yana yi mini ihun ni wanene da har zan yi masa ham, na san ko shi wanene?"

KU KARANTA: An kantarawa Naziru Sarkin Waka karya ta ban mamaki da ta sanya shi nuna fushin sa

Ya bayyana cewa akwai abokin aikin shi da suke tare a motar ya gudu ganin yadda jami'in dan sandan yake dukan shi.

Ya kuma bayyana cewa dan sandan ya fito da bindigar shi yayi harbi wajen da yake har sau biyu, mutanen da suka zo wucewa suke kallo sun nuna rashin jin dadin su akan abinda dan sandan yayi.

"Ya tafi ya barni na ja motata gefe, nayi tunanin abin ya zo karshe ashe ba haka bane, kawai sai ganin shi nayi ya dawo da motar 'yan sanda suka saka mini ankwa suka jefa ni a cikin motarsu suka wuce dani ofishin 'yan sanda dake Ikpai Omni mil 8 daga wajen da abin ya faru.

"A ofishin 'yan sandan yayi mini sharrin cewa na bata mishi mota, kuma na kira wasu mutane su dake shi.

"Bayan 'yan sandan sun bari nayi bayani kuma sunga cewa akwai ciwuka a jikina, sai suka sake ni cikin daren na wuce."

Mutumin ya nemi taimakon kungiyar kare hakkin dan adam, sannan ya wallafa wannan labari a shafinsa na Twitter, ko zai samu a bi masa hakkin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel