Rikita-rikita: Amarya ta haihu wata hudu kacal da yin aure a Kano

Rikita-rikita: Amarya ta haihu wata hudu kacal da yin aure a Kano

- Watanni su hudu kacal da yin aure amarya ta haihu

- Wannan lamari dai ya faru a karamar hukumar Minjibir dake jihar Kano inda aka kai lamarin kotu

- Angon ya bayyana cewa an damfare shi ne aka aura masa matar da an san cewa tana da juna biyu

Wata mai jego mai suna Maryam Bilal da madaurin auren ta Musa Khalil sun gurfana a gaban kotun majistratrate mai lamba 62, dake zaman ta a karamar hukumar Minjibir dake jihar Kano, karkashin mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, inda ake tuhumar su da hada kai da aikata laifi da kuma cutar da wani mutumi akan laifukan da suka saba wa sashi na cashi’in da bakwai da kuma na dari uku da ashirin da biyu, na kundin tafikadda shari’ar musulunci na jihar Kano.

Wani mutum ne dai mai suna Aminu Ibrahim, ya yi karar su a ofishin ‘yan sanda na Minjibir cewar Musa Khalil din ya aura masa Maryam alhalin tana dauke da juna biyu, kuma watan ta hudu da kwana ashirin da takwas ta haihu.

KU KARANTA: Allah daya gari ban-ban: Kabilar da samari ke kama 'yammata su yi musu dukan tsiya kafin a basu ita su aura

Koda Dan sanda mai gabatar da kara sajan Kabiru Bashir ya karanta musu kunshin tuhumar da ake musu, sai suka musunta. A nan ne mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, ya daga zaman zuwa ranar sha hudu ga wannan watan da mu ke ciki dan cigaba da sauraron karar.

Daga nan ne Lauyan da yake kare su ya roki kotun da ta bada belin su. Kuma kotun ta amince da rokon ta bayar da belin su, bisa sharadin mutane biyu masu kamala su tsaya musu sannan kuma su bada hotunan su na passport guda biyu a kotun, sannan kuma dan sandan kotun ya je ya gano gidajen su. In kuma wadanda akai belin suka tserewa shari’ah masu belin za su bada duba dari dari.

Rahotanni sun nuna cewa wani mutumi ne mai suna Sunusi Bala Alale ya yiwa Maryam wannan ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel