Dawafi 7x7 muka yiwa Ganduje kafin mu samu ya cire jar hular dake kan shi saboda kulle-kullen dake cikinta - Ali Baba

Dawafi 7x7 muka yiwa Ganduje kafin mu samu ya cire jar hular dake kan shi saboda kulle-kullen dake cikinta - Ali Baba

- Mun jima muna fama da Ganduje kafin mu samu ya cire jar hular dake kanshi mu huta

- Tsohon mai bawa gwamnan jihar Kanon shawara shine ya bayyana haka, inda ya ce kulle-kullen dake cikin jar hula ya fi karfin su domin kuwa suma dakyar suka samu suka cire ta

- Ya ce kowa sai da ya cire jar hula amma banda Ganduje, ko wanka idan zashi da ita yake shiga abin shi

Tsohon mai bawa gwamnan jihar Kano shawara a fannin addini, Hon Ali Baba a gama lafiya Fagge, yayi bayanin irin tsananin wahalar da suka sha kafin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya cire jar hular dake kanshi.

Jaridar Dabo FM ce dai ta ruwaito hirar da Ali Baba yayi da gidan rediyon Express dake Kanon Dabo tare da Salamatu Sabo Bakin-Zuwo.

Hirar da yayi ta nuna farin ciki ga kotun korafe-korafen zabe na tabbatar da nasarar da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi, Ali Baba ya bayyana jar hula a matsayin wani asiri da siddabaru da Kwankwaso yake yiwa masu sanya ta.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kauyuka muke bi ko zamu samu budurwar da zamu yiwa fyade tunda bamu da kudin da zamu nemi karuwai muyi zina da su - In ji Shafi'u Isah

"Cire Jar Hula ba abu bane mai sauki, muma sai da muka ta karanto Laqad Ja Akum, Li'ilafi, Ayatul Kursiyyu."

"Ko Ganduje kafin ya cire tashi daga kan shi sai da muka yi ta dawafi."

"Kowa a cikin mu ya cire Jar Hula, sai Ganduje, ko wanka zai shiga da ita yake shiga, ko ina da ita yake shiga a wajen dawafi ne kawai yake cirewa."

"Daga nan fa muka gane cewa jar hular dake kan Ganduje ta kama kanshi da yawa, mun gano cewa an fi kai tasa wajen mutanen Indiya, shine fa muka kara zage dantse wajen dawafi," in ji Ali Baba a gama Lafiya Fagge.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel