Hotuna: Tsofaffin jaruman Kannywood mata guda 15 da suka dawo harkar fim bayan mutuwar auren su
Kamar yadda muka ruwaito muku a rahoton dawowar jaruma Farida Jalal harkar fim, cewa yanzu kamar yayi ne ake na dawowar tsofaffin matan da suka taka rawa a masana'antar Kannywood, hakan yasa muka bincika muka zakulo muku wasu daga cikin jaruman Kannywood mata da suka taka rawar gani a baya a masana'antar ta Kannywood kana kuma bayan mutuwar auren su suka dawo harkar.
Koda yake wasu bamu da tabbacin sun dawo fim din ka'in da na'in kasancewar bamu gansu cikin fim ba amma akan gansu jefi-jefi cikin 'yan fim din, amma kuma da yawan su sun tabbatar da dawowar su inda wasu suka bayyana da bakin su wasu kuma kawai sai ganin su aka cigaba da yi a cikin fim.
KU KARANTA: Tirkashi: Saura kwana daya a daura auren su, ango yaje yayi fashi a banki saboda ya samu kudin da zasu sha hidimar biki da amaryar shi
Ga dai jerin jaruman a kasa:
1. Hadiza Kabara

Asali: Facebook
2. Hafsat Shehu

Asali: UGC
3. Fati Muhammad

Asali: Facebook
4. Maijidda Abbas

Asali: Facebook
5. Fati Baffa Fage

Asali: Facebook
6. Farida Jalal

Asali: Facebook
7. Rukayya Dawaiya

Asali: Facebook
8. Saima Muhammad

Asali: Facebook
9. Samira Ahmad

Asali: Facebook
10. Fauziyya Mai Kyau

Asali: Facebook
11. Sadiya Gyale

Asali: Facebook
12. Sadiya Kabala

Asali: Facebook
13. Maryam Ab Yola

Asali: Facebook
14. Tumba Gwaska

Asali: Facebook
15. Fati KK

Asali: Facebook
Maryam Ab Yola, Sadiya Kabala da Tumba Gwaska ba za a kira su da tsofaffin jarumai ba kasancewar ba wacce ta shekara goma a masana'antar a cikin su sai dai sun shiga wannan lissafi ne saboda sun yi aure kuma sun fito sun cigaba da harkar.
Haka zalika ba wai ana nufin wadannan sune kawai jaruman Kannywood mata da su kai aure suka fito ba amma sune ake kyautata zaton sun dawo harkar fim, kuma ana ganin su ne a cikin dukkan sha'ani na 'yan fim.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng