Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya

- Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya

- Budurwar mai shekara 18 a duniya mai suna Mangli Munda ta auri angonta karen mai suna Sheru

- Dangin amaryar dai sun yadda cewa idan har ta fara auren mutum to masifa da bala'i za su kewaye dangin su, hakan ne ya sanya dole sai ta fara auren kare sannan daga baya ta auri mutum

Wata budurwa 'yar shekara 18 a duniya dake kasar Indiya ta auri kare, an yi bikin wannan aure ne a gabashin jihar Jharkhand dake kasar ta Indiya.

Komai dai ya tafi yadda ya kamata, domin kuwa an yiwa amarya ado, an gayyato 'yan uwa da abokanan arziki, an rabawa sama da mutane saba'in abinci, sannan kuma an shirya wajen bikin kamar dai yadda aka saba.

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya
Mangli and Sheru
Asali: Facebook

Budurwar 'yar shekara 18 mai suna Mangli Munda ta auri mijinta kare mai suna Sheru. Manya a cikin danginta sun bayyana cewa idan har ta auri mutum namiji to tabbas za ta kawo musu bala'i cikin dangi, hakan ya sanya ta aurar karen.

KU KARANTA: Allah mai iko: Wani Kirista da yake zuwa Masallacin Juma'a yana shiryawa masallata takalmansu sannan yayi musu gadi

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya
Mangli and Sheru
Asali: Facebook

Sun yarda cewa idan har ta auri karen, to duk masifar dake bibiyarta za ta koma kan karen, hakan zai sa babu abinda zai faru da danginta bayan auren.

Da aka yi magana da ita, ta bayyana cewa kowacce mace tana da burin ganin ta auri wanda take so, kuma ta na da wannan burin, saboda haka za ta auri mutum nan gaba ba tare da kuma ta rabu da mijinta karen ba.

Ba wannan ne karo na farko da irin haka ta faru a kasar Indiya ba, inda a lokuta da dama akan samu aure tsakanin dabba da mutum, ko kuma mutum da itace ko bishiya.

Hotuna: Wata tsaleliyar budurwa ta auri kare a kasar Indiya
Mangli and Sheru
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel