Hotuna: Murna ta kaure yayin da Hauwa Indimi da mijinta dan gidan marigayi 'Yar'Adua suka haifi wani kyakkyawan yaro

Hotuna: Murna ta kaure yayin da Hauwa Indimi da mijinta dan gidan marigayi 'Yar'Adua suka haifi wani kyakkyawan yaro

- Bayan shekara daya da auren su, Allah ya albarkace su da kyakkyawan jariri namiji

- Hauwa Indimi da Mijinta Mohammed 'Yar'Adua sun samu karuwar ne a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar nan

- Hauwa ce dai ta sanar da samun karuwar ta su a shafinta na Instagram, inda ta sanya hotonta rungume da jaririn

Hauwa Indimi, diya a wajen hamshakin mai kudin nan na garin Maiduguri, Mohammed Indimi da mijinta Mohammed 'Yar'Adua, dan gidan marigayi tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Allah ya albarkace su da samun karuwar haifar kyakkyawan jariri namiji.

Hotuna: Murna ta kaure yayin da Hauwa Indimi da mijinta dan gidan marigayi 'Yar'Adua suka haifi wani kyakkyawan yaro
Hauwa and Mohammed
Asali: Facebook

Hauwa ce ta bayyana wannan labari a shafinta na sada zumunta na Instagram a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar 2019 dinnan. Ta sanya hotonta a lokacin da take rike da jaririn a hannunta, inda tayi rubutu kamar haka:

Hauwa and Mohammed
Hauwa and Mohammed
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yadda bera ya sanya 'yan majalisa gudun famfalaki a fadar shugaban kasar Amurka

Hotuna: Murna ta kaure yayin da Hauwa Indimi da mijinta dan gidan marigayi 'Yar'Adua suka haifi wani kyakkyawan yaro
Hauwa and Baby
Asali: Facebook

"Alhamdulillah, Allah ya albarkace mu da tsalelen yaro."

Idan ba a manta ba Hauwa da mijinta Mohammed 'Yar'Adua sun angwance shekarar da ta gabata, inda aka sha shagalin biki.

Hotuna: Murna ta kaure yayin da Hauwa Indimi da mijinta dan gidan marigayi 'Yar'Adua suka haifi wani kyakkyawan yaro
Hauwa and Mohammed
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel