APC ta jero wasu nasarori 6 da Buhari ya samu yayinda Najeriya ta cika shekara 59 da samun yanci

APC ta jero wasu nasarori 6 da Buhari ya samu yayinda Najeriya ta cika shekara 59 da samun yanci

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta taya kasar Najeriya murna akan zagayowar ranar yancinta karo na 59.

A wani jawabi daga kakakinta, Lanre Issa-Onilu, jam'iyyar ta bayyana cewa “Muna tunawa tare da yin jinjina ga iyayenmu wadanda suka yi yaki domin samun yancin kasarmu, mai girma kuma rundunan Sojinmu, da kuma tarin mutanen da suka sadaukar da rayukansu wajen kare martabar Najeriya da kuma tabbatar da hadin kan kasar.

“A matsayin kasa, za mu fi samun cigaba idan muna tare fiye da ace mun rabu. Saboda haka dole mu yaki wadanda ke buya karkashin inuwar addini, siyasa da kabilanci da masu kafa kungiyoyi don cusa mana kiyayya tsakaninmu. Duk da bambancinmu, karfinmu da cigabanmu zasu tabbata ne idan muka dogara ga aikinmu don cin amfanin junanmu."

Jam'iyyar ta jaddada cewa duk da tarin kalubalen da kasar ke fuskanta, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cimma nasara a wadannan bangarorin;

1. Yaki da cin hanci da rashawa

2. Habbaka tattalin arziki

3. Kakkabe ta’addanci da hana laifuffuka

4. Inganta kyawawan dabi’u a kasarmu

5. Karfafa hasashe da tsare-tsare damokradiyyarmu

6. Daukaka martabar kasar a idanun duniya

Ta kara da cewa “muna shawartan yan Najeriya na kwarai dasu yi ayyukan da zasu magance laifuffuka tare da inganta juriya, addini da kuma zaman lafiya a tsakanin mu, wanda hakan ne zai tabbatar da daukaka da cigaban Najeriya.

“A matsayin kasa wacce ke da mafi yawan al’umma a Afirka, zamu iya cimma manufofinmu, ganin irin arziki da albarkatun kasa da muke da shi. Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta jajirce wajen gina matsayin ta na Uwar Afrika.

"Muna taya dukkan yan Najeriya murnar zagayowar ranar yanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel