Ladabtar da yara ake yi a makarantar Kaduna ba azabtarwa ba – Kungiyar malaman Islamiyya

Ladabtar da yara ake yi a makarantar Kaduna ba azabtarwa ba – Kungiyar malaman Islamiyya

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar malaman makarantun Islamiyya karkashin jagorancin kungiyar Izala ta Rigasa da ke jihar Kaduna ta yi Allah-wadai samammen da aka kai makarantar tarbiyya da ke yankin.

Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa, Mallam Aliyu Adam, shugaban kungiyar malaman makarantun na Islamiyya karkashin kungiyar Izala ta Rigasa, ya ce suna goyon baya ga abubuwan da ake yi a cibiyar dari-bisa-dari.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna dai ta bayyana wurin da na bautar da bil adama ne, inda akasarin mutanen ciki suke daure da mari.

Tun farko dai rundunar 'yan sandan ta ce mutanen da aka kubutar sun kai 300 zuwa 500 amma yanzu mutane 190 aka mika wa Ma'aikatar Ayyukan kyautata Rayuwar bil Adama da Zamantakewa ta jihar.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta sake gurfana da wani sanatan Najeriya kan zambar N3.1bn

A baya mun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Alla-wadai da cin zarafin kananan yara a wani gida da jami'an 'yan sanda suka bankado a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna.

A wani jawaba da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Asabar a Abuja, shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da duk wani nau'in cin zarafin mutane, manya da kanana, ko take musu 'yanci.

Buhari ya yaba wa rundunar 'yan sanda bisa daukan matakan gagga wa bayan sun gano gidan. Kazalika, ya ce dole a bawa yara kariya daga duk wasu masu mugun nufi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel