Gwamnatin Zamfara ta sa ayi bincike akan batun sanya Qur’ani a najasa, tayi alkawarin bayar da naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai

Gwamnatin Zamfara ta sa ayi bincike akan batun sanya Qur’ani a najasa, tayi alkawarin bayar da naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai

Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wani bincike akan sha’anin da ke tattare da al’amarin tsintar wasu fallayen Qur’ani a najasa a makarantar Firamare a ranar Juma’a.

An gano shafukan littafin mai tsarki ne a makarantar Firamare na Shattima, Gusau, wanda yayi sanadiyar rufe makarantar har sai baba-ya-gani da kuma dakatar da malaman makarantar bisa ga umurnin gwamnan jihar, Alhaji Bello Matawalle.

Gwamnan wanda a yanzu haka ya halarci taron zuba jari na Afrika a kasar Amurka, ya umurci hukumar makarantar Firamare da ya kafa kwamitin bincike akan lamarin.

A wani jawabi daga babban sakataren gwamnati Alhaji Bala Maru, a Gusau a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, gwamnatin ta sanar da kafa kwamitin mutum 23, karkashin jagorancin Farfesa Jafaru Makau.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan fashi 3 sun hadu da ajalinsu a hannun fusatattun matasa a jihar Benue

Sauna mambobin kwamitin sune manyan malaman addinin Musulunci, wakilan hukumomin tsaro, ma’aikatu da abun ya shafa, cki harda kungiyar lauyoyin Najeriya.

Gwamnatin tayi alkawain bayar da kyautar naira miliyan 2 ga duk mutumin da ya kawo bayanai masu amfani.

Ya bukaci jama’a musamman a Gusau da su kai rahoton duk wani motsi da basu aminta dashi ba a kewayen su zuwa ga hukumar tsaro akan lokaci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel