Buhari ya jinjinawa Bill Gates da Dangote akan aikin alkhairin da suke yiwa yan Najeriya

Buhari ya jinjinawa Bill Gates da Dangote akan aikin alkhairin da suke yiwa yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba, 25 ga watan Satumba, ya jinjina wa gidauniyar Bill and Melinda Gates Foundation tare da gidauniyar Aliko Dangote akan taimako da ayyukan ci gaba da suke gudanarwa a Najeriya.

A wani jawabi daga hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba a Abuja, yace Buhari ya yi jinjinar ne a wata ganawa da yayi da attajiran biyu a gefen taron majalisar dinkin duniya na 74 a birnin New York, a ranar Laraba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa sun taba rayukan mutane da dama ta bangaren cigaba, sannan ya taya su murna “kan cimma abubuwan da suka shirya yi.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya tayi kaca-kaca da sasanin yan Boko Haram a Borno

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mutumin nan wanda ya fi kowa arziki a nahiyyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana babban fatan da ke cikin zuciyar sa na watan-watarana ya rinka sadaukar da dukiyarsa tamkar hamshakin mai kudin nan na duniya, Bill Gates.

Jaridar The Punch ta ambato Dangote yana fatan shi ma ya rinka fitar da wani babban kaso na dukiyar da ya mallaka ta kimanin dalar Amurka biliyan 9.2 wajen taimakon al'umma a doron kasa.

Dangote wanda alkalumma suka tabbatar da cewa ya fi kowane bakar fata kudi a duniya, ya bayyana wannan fata nasa ne a wani babban taro na bunkasa ci gaba a duniya na Goalkeepers’ event wanda gidauniyar Bill and Melinda Gates ta dauki nauyi a ranar Laraba cikin birnin New York na kasar Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel