Wani mutum ya kashe kansa a jihar Katsina

Wani mutum ya kashe kansa a jihar Katsina

Wani matashi mai shekaru 35 a duniya, Badamasi Musa, ya kashe ta hanyar rataya a kauyen Kabomo da ke karkashin karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an yi kacibus da gawar Badamasi tana reto a jikin wata itaciya da ke bayan gari a kauyen Kabomo, yayin da manoma ke kan hanyarsu ta zuwa gona da safiyar ranar Alhamis.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai, ya ce Badamasi yayin rayuwarsa yana fama da cuta ta tabin hankali da ya sanya ake zargin ita tayi ajalinsa.

A yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken diddigi, SP Gambo ya ce an riski gawar marigayi Badamasi rataye a jikin wata itaciya cikin wani jeji da ke kauyen Kabomo, lamarin da ya ce ana zargin ciwon zautuwar da yake damunsa yayi tasiri wajen debewa kansa tsammani.

KARANTA KUMA: Najeriya ta tafka asarar $157.5bn a tsakanin 2003 zuwa 2012 - Buhari

A wani rahoto na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, rayukan mutane 19 sun salwanta a yayin da fiye da mutane 300 suka jikkata, sanadiyar wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 5.8 da ta auku a Gabashin kasar Pakistan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel