Iko sai Allah: A karon farko 'yan Najeriya bakaken fata sun haifi jaririya baturiya

Iko sai Allah: A karon farko 'yan Najeriya bakaken fata sun haifi jaririya baturiya

- A lokacin da Angela Ihegboro ta fara ganin 'yar da ta haifa kasa magana tayi

- Yarinya ce 'yar baiwa, inji mahaifiyarta mai shekaru 35 a duniya

- Amma ni na kasa gane abinda ya faru a wannan wajen, in ji mai jegon

Abinda ya faru shine jaririyar wacce suka sanyawa suna Nmachi an haifeta da farin gashi da kuma shudin ido, inda hakan ke nufin bakaken fata sun haifi baturiya, mahaifan jaririyar 'yan asalin Najeriya ne suka koma birnin Landan da zama.

Abinda na fara cewa shine, "Menene ya faru?" in ji mahaifin yarinyar mai suna Ben Ihegboro. "Duka mun zauna ne mun saka ta a gaba muna kallon wannan ikon Allah bayan an haifo ta, mun kuma kasa cewa komai."

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kone yaro Musulmi dan shekara 15 a Indiya saboda yaki komawa addinin Hindu

"Kwarai kuwa 'yata ce, na yadda da mata dari bisa dari," inji mahaifin yarinyar mai shekaru 44 a duniya.

Masana dai ba su yadda wannan mu'ujizar ba, sai dai kuma basu da wata shaida dake nuna cewa yarinyar ba ta su bace, sai dai duk da haka ba su yi shiru da bakinsu ba, domin kuwa sai da suka kawo misalai guda uku akan wannan lamarin.

Amma sai dai kuma wasu mutanen suna ganin kamar akwai lauje cikin nadi a wannan lamarin, ma'ana suna so mijin ya binciki matar duk kuwa da yace ya yarda da ita dari bisa dari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel