Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Gobara ta yi ajalin jarirai 8 a wani asibitin Algeriya

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Gobara ta yi ajalin jarirai 8 a wani asibitin Algeriya

Hukumar tsaro ta kasar Algeriya ta bayyana cewa akalla jarirai takwas ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibitin kasar a ranar Talata, 24 ga watan Satumba.

A cewar hukumar, Gobarar ta faru ne da safiyar yau Talata a asibitin da ke Yankin Oued Souf, wani yanki mai tazarar kilomita 700 a yankin kudu maso gabashin babban birnin Algiers.

Hukumar tace Jariran sun mutu ne sanadiyyar kuna da kuma shakar hayakin gobarar, inda ta kara da cewa an ceto wasu jarira 11 da mutane 65 wadanda suka hada da mata 37.

A 2018 ne gobara ta tashi a asibitin, wanda yayi sanadiyyar konewar mafi akasarin sassan asibitin.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Hafsat Idris tayi bikin samun mabiya miliyan daya a shafin Instagram

A wani labari na daban, mun ji cewa Hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya NSCDC, ta cafke wani mahaifi mai shekaru 46, Muhammad Pantami, da laifin zakkewa diyarsa budurwa 'yar shekaru 15 a jihar Borno.

Kwamandan hukumar NSCDC reshen jihar Borno, Abdullahi Umar, shi ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Kwamandan hukumar yana cewa, Pantami ya shiga hannu ne a ranar 29 ga watan Agustan da ya gabata cikin yankin Balabulin-Allajeri da ke wajen birnin Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel