Tirkashi: Iya wadanda ke da digiri a dakikanci da rashin hankali ne kawai zasu bar PDP su koma APC - Dino Melaye

Tirkashi: Iya wadanda ke da digiri a dakikanci da rashin hankali ne kawai zasu bar PDP su koma APC - Dino Melaye

- Fitaccen Sanatan nan dan barkwanci na jihar Kogi, Sanata Dino Melaye yayi wata magana dangane da masu canja sheka daga PDP zuwa APC

- Sanatan ya bayyana cewa iya mutanen da suke cikakkun dakikai ne kawai zasu canja sheka daga jam'iyyar PDP su koma jam'iyyar APC

- Sanatan ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC kamar ta sha kasa ne a zaben gwamnan da za ayi a jihar Kogi a watan Nuwamban nan mai zuwa

Sanatan jihar Kogi ta Yamma wanda aka dakatar daga kujerar shi makonnin da suka gabata, kuma wanda ya sha kasa a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi a jam'iyyar PDP, wato Sanata Dino Melaye, yayi wata magana akan mutanen da suke canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Sanatan ya bayyana cewa iya mutanen da suke da digiri a rashin hankali da kuma masu difloma a dakikanci ne kawai za su iya sauya sheka daga jam'iyyar PDP su koma jam'iyyar PDP.

Haka kuma Sanatan ya kara da tabbatar da cewa dole ne jam'iyyar PDP ta kayar da jam'iyyar APC a zaben gwamnan da za ayi a jihar Kogi a watan Nuwamban nan mai zuwa.

KU KARANTA: Dan hakin da ka raina: Yayi kokarin yaci zalinta, ashe 'yar dambe ce bai sani ba, ita kuwa tayi ta jibgarsa kamar Allah ne ya turo ta

"Iya cikakkun dakikai da kuma wadanda suke da digiri a rashin hankali ne kawai za su bar jam'iyyar PDP su koma APC. Jam'iyyar APC kamar ta sha kaye ne a jihar Kogi," Sanatan ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne muka kawo muku labarin yadda Sanatan ya fito ya karyata jita-jitar da ake yadawa a shafin Twitter na cewa yayi alkawarin zai bayar da motoci guda goma idan har dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kayar da shugaba Buhari a kotu.

Sanatan ya bayyana cewa shi babu wanda ya yiwa wannan alkawari, hasali ma shafin da aka wallafa wannan rubutu ba nashi bane, na bogi ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel