Wani matashi ya kashe gwaggonsa mai kusunbi don yin asiri

Wani matashi ya kashe gwaggonsa mai kusunbi don yin asiri

Rundunan yan sanda reshen jihar Ebonyi ta kama wani mai suna Eric Ifeanyi Okoro da ake zargi da damfara ta yanar gizo da kuma kashe gwaggonsa mai kusunbi wacce aka ambata da suna Benisa Okoro.

An rahoto cewa mai laifin wanda al’umman Umuka a kauyen Okposi suka fi sani da 'yahoo boy', ya dawo gida cikin dare, ya ci abincin da gwaggonsa ta ajiye masa kafin ya daba mata wuka a kirji har sai da ta mutu.

An fahimci cewa direban dakin ajiye gawa na babban asibitin da ya tuntuba don daukar gawan gwaggwonsa zuwa asibibitin ya ki amincewa da bukatarsa ganin yanda jini ke kwarara. An kama Eric ne bayan direban yayi kururuwa, inda ya jawo hankali sauran mazauna kauyen.

Majiya sunce bai musanta kisan ba ya kuma amsa laifinsa sannan kuma har ila yau ya bayyana cewa mahaifinsa da yayi yunkurin kashewa a Owo, jihar Ondo ne mutum na gaba wanda zai kai ma hari.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta aika sammaci ga Okorocha akan zargin take doka

Yayin da yake tabbatar da lamarin, Shugaban kungiyar matasan Umuka, Nwanneka Ngada Okorie yace dan damfaran ya kasance mutum mai son ace abubuwa na gudana yanda yake son su gudana.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah yace ana gudanar da bincike kan al’amarin kuma za a gurfanar da mai laifin a kotu baya an kammala binciken.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel