Sakon taya murna da nayi wa Buhari daga zuciyana ya fito - Wike

Sakon taya murna da nayi wa Buhari daga zuciyana ya fito - Wike

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da yasa ya keta dokar jam’iyya don taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

Wike yace ya bayyana sakon taya murna ga Shugaban kasar a bainar jama’a ne saboda “hakan ya zo ne daga zuciya”.

Gwamnan yace sakon taya murnarsa da ya yi a bude ya yafi wanda takwarorinsa suka yi inganci, "ba irin na wasu gwamnonin PDP da suka bi dare suka ziyarci shugaban kasar ba."

Wike ya bijire ma jam’iyyar shi a ranar Laraba, 11 ga wata Satumba, a lokacin da ya gabatar da wasikar taya murna zuwa ga shugaban kasa a daidai lokacin da jam’iyyarsa ta bayyana shirinta na cigaba da kalubalantar zaben shugaban kasa Buhari a kotun koli.

Ya isar da sakonsa ne a wani jawabin da mataimakinsa na musamman kan kafofin yada labarai, Mista Simeon Nwakaudu ya gabatar.

Idan za ku tuna PDP da dan takaranta, Atiku Abubakar sun nufi kotun dake sauraran karan zaben shugaban kasa a Abuja, inda suka bukaci soke nasaran da Buhari yayi a zaben 23 ga watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA KUMA: Nasarar Buhari a kotu: Manyan lauyoyi sun jinjinawa kotun zabe saboda wannan hukunci

Amman yayin da yake yanke hukunci akan lamarin Justis Mohammed Garuba yayi watsi da dukkan kararrakin.

Gwamnan ya bukaci Buhari da yayi amfani da nasaran da ya samu wajen yiwa yan Najeriya aii, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel