An fada mani 50% na kudin kwangila asusun Gwamna yake komawa - Makinde

An fada mani 50% na kudin kwangila asusun Gwamna yake komawa - Makinde

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya koka da yadda wasu daga cikin masu mulki a jiharsa ke wawurar kudin al’umma. Gwamnan na PDP ya bankado yadda aka rika satar kudin kwangila.

Seyi Makinde ya ce an fada masa cewa kashi 10% na kudin da aka warewa kwangila ne kurum yake tafiya wajen ainihin aikin. Gwamnoni da Iyalansu kan yi wawaso ne kan ragowar kudin.

Mai girma Gwamna Makinde yake cewa gwamna da Mai dakinsa da kuma ‘Dan siyasa da ya kawo kwangila ne su ke tashi da kudin kwangilar. Wannan ya sa ya sha alwashin yin bincike a jihar.

Gwamnan ya fito shafinsa na Tuwita ne yana tonawa masu mulki a jihar na sa asiri da cewa gwamna kan dauki kashi 50% na duk wani kudin aikin kwangila, sai a ba Matarsa kuma 10%.

Haka zalika kashi 30% na kudin da aka ware domin aiki su kan kare ne a cikin aljihun jami'in da ya kawo kwangila a jihar. Abin da hakan ke nufi shi ne kashi 10% rak ne zai tafi wajen aikin.

KU KARANTA: Ana rade-radin an bada umarni a kama wani tsohon Gwamnan APC

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnan ya fara yin wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da Manema labarai a gidan Talabijin na jihar Oyo watau BCOS TV bayan ya cika kwana 100 a ofis.

Sabon gwamnan yake cewa ya bayyana kadarorinsa a gaban Duniya ne domin jama’a su yi masa hisabi. Gwamnan na PDP ya rantse sai ya yi maganin wadanda su ka rika barna da dukiyar jihar.

Injiniya Makinde ya karbi mulki ne daga hannun jam’iyyar APC a jihar Oyo a zaben 2019. Gwamnan ya kuma bayyana yana na da tarin biliyoyi na dukiya wajen tsabar kudi da kadarori.

Gwamnan ya ce: "Mulki na gari ya sha gaban siyasa, dole duk 'dan kwangilar da a ka biya kudi ya karasa aikinsa. Kamar aikin rumbun da na gani bai burge ni ba. Haka kwangilar gidan gwamnati'

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng