Hamshakan kananan yara masu kudi da ba su haura shekara 30 ba

Hamshakan kananan yara masu kudi da ba su haura shekara 30 ba

Legit.ng Hausa ta kawo maku yaran da su ka shiga cikin manyan Attajiran Duniya. Wasunsu sun samu kudi ne ta kwarewa fasaha,abinci, ko na’urorin zamani ko kuma bangaren jirgin sama.

A shekarun baya da su ka wuce, fitaccen Mai kudin nan, Mark Zuckerberg, Mai kamfanin Facebook, yana cikin jerin inda ya zama hamshakin Mai kudi tun yana shekara 23 a Duniya.

1. Alexandra Andresen

Alex Andresen mai shekaru 22 da haihuwa ce ta farko a wannan jeri. An haife ta ne a 1996 a kasar Norwegia. Mahaifinta Johan H. Andresen, shi ne mai kamfanin nan na Ferd wanda su ka gada.

2. Katharina Andresen

Katharina Andresen watau ‘Yaruwar Alex Andresen ita ce ta biyu a jerin Attajiran yara a Duniya. Katharine wanda ita ma ta mallaki Dala biliyan 1.4 kamar Alex, ta na da shekaru 23 ne a ban kasa.

KU KARANTA: Wadume ya bayyana yadda ya samu kudin da kowa ya ke magana

3. Gustav Magnar Witzoe

Gustav Magnar Witzoe shi ne wanda ya ke da kusan rabin kamfanin SalMar. Matashi Magnar Witzoe, mutumin kasar Norway ne kuma ya yi arziki ta sanadiyyar kamfanin Mahaifinsa.

4. Evan Spiegel

Evan Spiegel shi ne ya fado a na hudu a wannan jeri na shafin Investopedia. Speigel ya ba Dala biliyan 2.2 baya, kuma shi ne mai kamfanin nan na Snap Inc. masu kula da manhajar SnapChat.

5. Ludwig Theodor Braun

Ludwig Braun wanda ya ke da shekara 28 shi ne na karshe a wannan jeri na mu na mutane biyar. Braun ya yi arziki ne da wani kamfanin da ke yin kayan kiwon lafiya mai suna Braun Melsungen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel