Rana irin ta yau a tarihi: Jihohi 9 da aka kirkira ranar 27 ga watan Agusta

Rana irin ta yau a tarihi: Jihohi 9 da aka kirkira ranar 27 ga watan Agusta

A rana irin ta yau ne, 27 ga watan Agusta, aka kirkiri sabbin jihohi guda tara a Najeriya, lamarin da ya kara yawan jihohin Najeriya zuwa 36. Yanzu haka an samu shekaru 28 cif-cif da kirkirar jihohin.

Jihohin 9 da aka kirkira a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1991 sune:

1. Adamawa state

2. Taraba state

3. Enugu state

4. Edo state

5. Delta state

6. Yobe state

7. Kebbi state

8. Osun state

9. Jigawa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ne ya kirkiri jihohin a shekarar 1991.

Tun a ranar 26 ga watan Agusta, Legit.ng ta wallafa labarin cewa domin tunawa da shekaru 28 na samuwar jihar, gwamnatin Jigawa ta bai wa ma'aikatan ta hutu a ranar Talata, lamarin da ta ce su shakata kuma su yi wa jihar addu'o'i na samun aminci.

Sanarwar kaddamar da hutun ta zo ne a cikin wani sako da sa hannun kakakin ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Isma'il Ibrahim, wanda ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin birnin Dutse.

DUBA WANNAN: Daga karshe: Hukumar kwastam ta yi magana a kan rufe iyakokin Najeriya a jihohin arewa uku

"Gwamnatin Jigawa tana taya dukkanin al'ummar jihar murnar zagayowar wannan rana, kuma tana fatan za su ribaci wannan lokaci wajen kwarara addu'o'i ga jihar da kuma kasa baki daya."

"A yayin haka kuma, gwamnatin jihar tana fatan dukkanin ma'aikata za su ribaci wannan lokaci na hutun kwana daya da suka samu wajen yi wa Allah godiyar wanzar da zaman lafiya a jihar da kuma ayyukan ci gaba na inganta jin dadin al'umma da gwamnatin jihar ke ci gaba da aiwatarwa."

"Kazalika gwamnatin tana jajantawa 'yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya da kuma sauran wadanda dukiyoyinsu suka salwanta a sanadiyar ambaliyar ruwa da ta auku a jihar da kuma wasu jihohi a kasar nan."

"Gwamnati tana fatan mutanen jihar mu za su ribaci kashedin da hukumomi masu ruwa da tsaki suka yi masu a kan hanyoyin dakile aukuwar ambaliyar ruwa a lokuta na gaba," inji Alhaji Isma'ila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng