Kaftin Tijjani Balarabe: Ku sadu da jami'in sojan da ya ubutar da Wadume daga hannun 'yan sanda

Kaftin Tijjani Balarabe: Ku sadu da jami'in sojan da ya ubutar da Wadume daga hannun 'yan sanda

Tun bayan bayyanar harkallar kubutar da gawurataccen mai garkuwa da mutane, Hassan Bala Wadume, suna da hotunan Kaftin Tijjani Balarabe suka mamaye kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta.

A ranar Lahadi ne jaridar Legit.ng ta ci karo da wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa cikin harshen turanci a kan tarihin rayuwar kaftin Tijjani Balarabe tun daga haihuwa har zuwa shigarsa aikin soja da yadda yake gudanar da rayuwarsa kafin sunansa ya shiga bakin duniya.

Mahiafinsa, dan asalin jihar Kano, malamin addinin Islama ne a unguwar Tudun Fera da ke yankin karamar Jos ta Arewa a jihar Filato, kuma a nan Tijjani ya taso tare da sauran tsaransa.

Bayan ya kammala makarantar sakandire a shekarar 1990, Tijjani, wanda aka fi kira da 'Teejay ko Tijjani 'Dan Fari', saboda yana da haske, ya kasance mai matukar kaunar buga wasan kwallon kafa kafin sakamakonsu na jarrabawa ya fito.

Tijjani na daga cikin matasan da suka samu aikin soja yayin da rundunar soji ta dauki aiki a shekarar 1992/1993 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida.

Wasu masu kusanci da Tijjani sun bayyana cewar bai cigaba da karatu ba tun bayan kammala makarantar sakandire, amma sun bayyana cewa yana da matukar sa'a a cikin aikin soja, saboda ya yi aiki da manyan jami'an sojoji a wurare daban-daban.

Wani jami'in soja ya bayyana cewa a shekarar 2000 ne Tijjani ya cike takardar neman zama babban jami'in soja, kuma har aka kira shi makarantar horon sojoji da ke Jaji domin a tantance shi tare da sauran masu neman karin girma.

Jami'in sojan ya kara da cewa amma koda aka duba takardun Tijjani sai aka fahimci cewar takardar sakandiren da ya gabatar ba ta shi ba ce, lamarin da yasa aka kulle shi. Sojan ya ce, shi kansa bai san yadda aka yi daga baya maganar ta mutu ba, har aka saki Tijjani.

Amma duk da faruwar hakan Tijjani bai hakura ba don sai da ya kara neman karin girma a shekarar 2013, kuma ya yi sa'a ya samu a lokacin.

Bayan ya kammala karbar horo ne aka tura shi yankin arewa maso gabas domin yakar aiyukan kungiyar Boko Haram.

Wasu abokan Tijjani sun bayyana cewa tabbas sun ga canji a halayyyarsa tare da nuna 'ji-ji da kai' a wurinsa musamman bayan ya warke daga wata jinyar harbin da aka yi masa yayin wani ofireshon.

Abokan sun kara da cewa basu wani damu da lamuran rayuwar Tijjani ba, wasu ma sun manta da shi sai bayan da faruwar harkallar Wadume da sunansa da hotuna suka mamaye dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai.

A ziyarar da wakilin jaridar Daily Trust ya kai unguwar Tudun Fera, inda aka haifi Tijjani, ya ga sabon gidansa da ya gina da kuma wani wuri da yake gina gidan biredi.

Waja majiya ta bayyana cewa Tijjani na shirin shigo da wasu na'urori daga kasar waje domi fara aiki a gidan biredin a daidai lokacin da badakalar Wadume ta bullo.

Tuni shugaban rundunar soji ya bayar da umarnin tsare Tijjani tare da ragowar sojojin da ya bawa umarnin su kubutar da Wadume daga hannun 'yan sandan da suka kama shi a ranar 6 ga watan Agusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel