Faduwar gaba asarar namiji: Ni zan yi nasara a kotun daukaka kara - Dino Melaye

Faduwar gaba asarar namiji: Ni zan yi nasara a kotun daukaka kara - Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye mai wakiltar jihar Kogi ta yamma ya bayyana cewa wannan hukunci da kotu ta yanke a kanshi ko a jikinshi

- Saboda ya san cewa dole idan an koma kotun daukaka kara shine zai yi nasara, saboda haka yake cewa mutanensa su kwantar da hankalinsu

- Ya bayyana cewa kuma dama koda ma haka ba ta faru ba dole sai an sake yin zaben Sanata kogi ta yamma domin kuwa shine zai zama gwamnan jihar Kogi idan an yi zabe

Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa hukuncin da kotu ta zartar na cewa sai an sake gabatar da zaben kujerarsa ta Sanata bai dame shi ba ko kadan.

Dino ya kara da cewa dama tun farko koda ace shine wanda yayi nasara a zaben to dole sai abokin karawarrsa ya kai kara kotu.

"Ina kira ga dukkanin magoya bayana da su kwantar da hankalinsu, na san cewa dole nasara tana gare mu. Wannan hukunci da aka yanke bai dame ni ba ko kadan, kuma na san cewa ko munje kotun daukaka kara mune da nasara.

KU KARANTA: Tabbas ni na saka 'yan sanda suka kama Sadiya Haruna har sai da ta bada hakuri - In ji Teema Makamashi

"Sannan kuma koda ma ace haka ba ta faru ba dole sai an sake yin zaben Sanata na jihar Kogi ta yamma saboda nine zan lashe kujerar gwamnan jihar Kogi."

Idan ba a manta ba yau ne kotu ta soke zaben Sanata Dino Melaye da yake wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya.

Hukuncin wanda Sanata Smart Adeyemi ya kai kara ya bayyana cewa wannan zabe da aka yi a jihar babu gaskiya ko kadan a cikin shi, saboda haka dole ne a sake zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel