2023: Buhari ya kafa 'yan siyasar da za su lallasa PDP a Kudu maso Kudu

2023: Buhari ya kafa 'yan siyasar da za su lallasa PDP a Kudu maso Kudu

Bayyanar wasu manyan 'yan siyasa hudu cikin jerin ministoci 'yan majalisar zartarwa da suka fito daga yankin Neja Delta, ta bayyana manufar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta janyo ra'ayin al'ummar yankin zuwa jam'iyyarsa ta APC.

Majiyoyin rahoto masu tabbas na jam'iyyar APC a ranar Asabar sun shaidawa manema labarai na jaridar Vanguard cewa, tunkahon da babbar jam'iyyar adawa a kasar PDP ke yi a yankin Neja Delta zai zamo tarihi a shekarar 2023.

Babban dalilin wannan bugun kirji na jam'iyyar bai wuci yadda gwamnati mai ci a kasar ta kafa wasu manyan siyasa hudu da suka fito daga yankin domin yiwa PDP rubdugu da taron dangi a babban zaben kasa na 2023.

Manyan 'yan siyasar hudu da za su jagorancin ayarin yaki na jam'iyyar APC domin cimma nasara a yankin Neja Delta sun hadar da; Sanata Godswil Akpabio, Rotomi Amaechi, Festus Keyamo da kuma Timipre Sylva.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, bayan kasancewar wasu daga cikin su tsaffin gwamnoni, dukkanin wannan gwarazan 'yan siyasa hudu sun kasance ministoci a majalisar zartarwa ta shugaban kasa Buhari da za su yi tasirin gaske wajen lakacewa PDP hanci tare da tsige tutocinta a 2023.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta ci gidaje a Jigawa

Manyan 'yan siyasar hudu yayin gabatar da jawabansu bayan karbar rantsuwa da kujerar minista, sun yi tarayya da juna cikin yakini na jaddada kudirin tabbatar da jam'iyyar APC ta samu gindin zama a jihohinsu.

Ga dai jihohi da kuma yadda mukamai na madafan iko da manyan 'yan siyasar hudu suka samu a gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Buhari kamar haka:

Akwa Ibom: Sanata Godswill Akpabio - Ministan Neja Delta

Bayelsa: Timipre Sylva (Tsohon gwamnan jihar Bayelsa) - Karamin ministan man fetur

Ribas: Rotimi Amaechi (Tsohon gwamnan jihar Ribas) - Ministan Sufuri

Delta: Festus Keyamo - Karamin Ministan Neja Delta

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel