Tirkashi: Idan na cika shekara 40, zan auri maza 3, na gina musu gidaje sai na dinga zabar wanda zan kwanta da shi a cikinsu - Toyin Lawani

Tirkashi: Idan na cika shekara 40, zan auri maza 3, na gina musu gidaje sai na dinga zabar wanda zan kwanta da shi a cikinsu - Toyin Lawani

- Toyin Lawani ta yi wata magana da ta karawa sama hazo matuka a shafinta na Instagram

- Toyin ta bayyana cewa idan ta cika shekara arba'in za ta auri maza guda uku ta yi kuma yadda take so da su

- Ta ce idan lokacin yayi za ta ginawa kowanne a cikinsu gida, sannan za ta dinga zabar wanda za ta kwanta da shi a cikinsu, yayin da kuma za ta kora sauran daukunansu

Toyin Lawani ta sanya alamar tambaya akan dokar da ta sanya cewa maza za su iya aurar mace fiye da guda daya, amma kuma ta hana mata auran maza da yawa.

Yanzu dai Toyin ta bayyana cewa za ta auri maza guda uku idan ta cika shekara arba'in a duniya, saboda idan har an bar namiji yayi haka ita ma za ta iya yi.

A cewarta, za ta gina gidaje ga kowanne namiji da za ta aura, sannan kuma zata gina wani gida daban wanda zai zama inda mazajen zasu dinga zuwa suna kwanciya da ita idan lokacin kwanciyarsu yayi.

Ta cigaba da gayawa maza cewa yanzu duniya ta canja mata zasu iya yin duk wani abu da namiji zai yi, amma kuma ba kowanne abu bane namiji zai yi da mace take yi, inda ta yi amfani da daukar ciki a matsayin misali.

KU KARANTA: Babbar magana: Idan 'yan Hausa fim 'yan wuta ne to kowa ma dan wuta ne - In ji Ibrahim Mu'azzam

Ga abinda ta rubuta a shafinta na Instagram:

"Mene yasa maza za su iya aurar mata da yawa, amma mata ba za su iya ba? Idan na cika shekara 40 zan auri maza uku da kudina, zan ginawa kowanne a cikinsu gida, sannan zan dinga zabar duk wanda nake so na kwanta dashi a cikinsu a lokacin dana ga dama, sannan sauran zasu tafi dakunansu."

Ta kara da cewa: "Idan na aureka idan ka ga dama kada kayi mini biyayya, zan sake ka na auro wani wanda zai yi mini biyayya, dole a dinga daraja mata a duniya yanzu, maza basu iya haihuwa ba, kuma na san cewa mata baza su iya haihuwa ba sai da maza, amma zamu iya zuwa mu siyo maniyi mu sha."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel