Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna na dimbin dukiya a Jihar Niger

Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna na dimbin dukiya a Jihar Niger

Rahotanni sun kawo cewa anyi asarar dimbin dukiya da gidaje masu yawa a garin Minna, babbar birnin jihar Niger, sakamakon ballewar ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya haddasa ambaliyar ruwa.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Niger, Ahmed Inga ne ya tabbatar da haka a ranar Asabar, 17 ga watan Agusta, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kan ambaliyar.

Inga ya bayyana takaicin cewa kashi 75 bisa 100 na ambaliyar ta faru ne dalilin zubar da shara karazube da jama’a ke yi.

Hakazalika ya bayyana cewa yadda mutane ke yawan gina gidaje da shaguna a kan hanyoyin ruwa na daya gada cikin abubuwan da ke haddasa afkuwar ambaliyar ruwan.

Ya kuma jadadda cewa hukumar sa ta sha jan kunnen jama’a akan su guji zubar da shara barkatai domin ta na toshe magudanan ruwa. Kuma su daina yin gine-gine a kan hanyar ruwa.

Ya karyata rade-radin cewa tumbatsar da ruwan dam din Bosso ta yi ne ta haddasa ambaliya a gidajen jama’a.

Dangane da mutane uku da ake yada ji-ta-ji-tar sun halaka a cikin ambaliyar, Inga ya ce ba su da tabbacin salwantar ratukan na su, amma ana bincike domin tantancewa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Wata mota kiras bas ta gamu da hatsari a kan hanyar Kano daga Taraba

Mukaddashin gwamnan jihar Niger, Ahmed Ketso, ya kai ziyara wajen da lamarin ya afku, inda ya nuna jimami kuma ya ce gwamnatin jiha na da niyyar gina karin magudanan ruwa da kwalbatoci masu yawa.

Wani mai suna Abubakar Mamman, ya ce da idon sa ya ga ruwa ya ciwo wata mata ta na ta kururuwar neman agaji.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel