Tazarce: Hajiya Ummi El-Rufai ta shirya taron godiya na kwanaki a Garuruwan Kaduna

Tazarce: Hajiya Ummi El-Rufai ta shirya taron godiya na kwanaki a Garuruwan Kaduna

Daya daga cikin Matan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai watau Aisha Ummi Garba El-Rufai, ta sake godewa mutanen jihar da su ka zabi Mai gidan a matsayin gwamna karo na biyu.

Hajiya Ummi El-Rufai ta ke cewa mutanen Kaduna ba za su ciza yatsa a game da sake zaben gwamnan na su ba. Mai dakin gwamnan na APC ta ce gwamnatin nan za ta cika alkawuran da ta yi.

Aisha Garba watau Ummi El-Rufai ta yi wannan bayani ne a cikin karamar hukumar Igabi inda ta fara wani taron gangami ta na godewa al’ummar jihar na sake marawa APC baya a zaben da a ka yi bana.

The Guardina ta rahoto cewa Ummi El-Rufai za ta shafe kwanaki hudu ta na wannan zagayen gari. Yanzu dai Matar gwamnan ta shiga Yankin Jaji, Afaka, Rigachikun, da Barakallahu da ke cikin Igabi.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, shi ne ya tarbi Mai dakin gwamnan a gidansa da ke Rigachikun. Yusuf Zailani ya dauki lokaci ya yabawa gwamnatin El-Rufai.

KU KARANTA: Yadda Gwamnati ta ajiye Zakzaky da Mai dakinsa a cikin GRA a Kaduna

‘Dan majalisar na Igabi ya jawo hankalin gwamnatin APC da ta habaka harkar noma da kuma ba mata jari domin su fara kasuwanci tare da fadada wasu hanyoyi da kuma gina asibiti a Garin Rigachikun.

Matar gwamnan ta cika alkawarin da ta yi na cewa za ta sake ziyartar wadannan wurare ta yi masu godiya da zarar APC ta samu nasara a zabe. APC ce ta kuma samu gagarumar nasara a Kaduna.

A Garin Jaji, Hakimin Rigachikun, Abdurrasheed Sani, da mutanensa sun ji dadin wannan ziyara da Matar gwamna ta kawo masu. Hakimin ya yi kira ga gwamnati ta duba kiwon lafiya da aikin yin Matasa.

A Unguwar Afaka, Mai Garin da kan shi, Sani Umar da wasu mutanensa ne su ka tarbi Hajiya El-Rufai. Mutanen Afaka sun yabawa gwamnatin Jihar na bada aikin hanyar Mashi Gwari zuwa Rigasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel