A cikin wani katafaren gida a ka ajiye mu ba a kurkuku ba – Zakzaky

A cikin wani katafaren gida a ka ajiye mu ba a kurkuku ba – Zakzaky

Jagoran kungiyar IMN ta ‘Yan Shi’a a Najeriya, Ibraheem El-Zakzaky, ya bada dalla-dallar labarin halin da shi da Iyalinsa su ke ciki a kasar a lokacin da ya je Indiya neman magani kwanan nan.

A wani bidiyo da jaridar The Cable ta fitar, an ji Jagoran na Mabiya addinin Shi’a ya na ba wani jami’in gwamnatin kasar Indiya labarin inda gwamnati ta tsare sa tare da Mai dakinsa akasin abin da a ke ji.

“Na yi kusan shekaru hudu a gidan kaso; a wani katafaren gida na ke. Kai bari ma, makwabcinmu shi ne shugaban majalisar dattawa; a wannan katon gida. Na samu damar watayawa a gidan...

...Haka zalika a lokacin da su ka dauke ni zuwa Kaduna, a mafi kyawun wuri na ke – Unguwar GRA. A nan ma wani gida ne cike da kaya da manyan Dakuna, kuma ina da cikakken sarari...

...Ba a taba tsare ni cikin ‘Yan Sanda ba; A’a, Sojojin da ke nan, su na tsayawa ne a wajen gida. Haka su ke yi. A lokacin da mu ka zo nan (Indiya) tamkar gidan kurkuku a ka garkame mu." Inji Zakzaky.

KU KARANTA: Abin da ya sa mu ka dawo da Zakzaky gida - Inji Gwamnati

Wannan labari da Shehin Malamin ya bada akasin abin da jama’a su ke tunani na cewa babban Jagoran Shi’ar ya na tsare ne a cikin gidan yari garkame tare da Mai dakinsa tun karshen Disamban 2015.

Zakzaky ya bada wannan labari ne ga wannan jami’in kasar waje wanda a ka gani a gefen gadonsa lokacin da ya ke asibitin Indiya domin a duba shi. Daga baya hakan bai yiwu ba, har ya dawo gida.

A wani lokaci gwamnatin tarayya ta taba ikirarin cewa duk wata ta na kashe sama da Naira miliyan 13 a kan kula da Ibrahim Zakzaky. Lai Mohammed ne ya yi wannan magana wanda ya jawo surutu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel