Buhari ya koma garin Abuja bayan kammala hutun sallah a Daura

Buhari ya koma garin Abuja bayan kammala hutun sallah a Daura

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar 17 ga watan Agusta, ya tattara inasa-inasa ya koma babban birnin kasar na Abuja bayan kammala hutunsa na babbar sallah a mahaifarsa ta garin Daura dake jihar Katsina.

Buhari yayin saukarsa a yau Asabar cikin birnin Abuja
Buhari yayin saukarsa a yau Asabar cikin birnin Abuja
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya yi sallama da filin jirgin saman kasa-da-kasa na Umaru Musa 'Yar'Adua dake birnin Katsinan Dikko da misalin karfe 11.00 na safiyar ranar Asabar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da ya ke hutunsa na bikin babbar sallah a garin Daura, shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin manyan baki da suka hadar da takwaransa na kasar Guinea, Alpha Conde, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan tare da mataimakinsa, Ovie Omo-Agege, gwamnonin Najeriya 12 da sauransu.

Kazalika shugaban kasar ya kai ziyarar jaje a kananan hukumomi bakwai na jihar Katsina da ta'addancin 'yan daban daji ya fi jefa su cikin halin ni 'yasu. An yi dandazon karbar gaisuwar Buhari a karamar hukumar Batsari.

Baya ga haka shugaban kasar ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka na ci gaba da gwamnatin jihar Katsina ta aiwatar karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari. Ya kuma jagoranci bude katafaren asibitin rundunar dakarun soji sama a garin Daura.

KARANTA KUMA: Kafin Kirsimeti za mu shigar da kasafin kudin 2020 cikin doka - Sanata Lawan

Ana iya tuna cewa shugaba Buhari ya tashi daga birnin Abuja zuwa Katsina a ranar Juma'a 9 ga watan Agusta, domin gudanar da bikin babbar sallah cikin 'yan uwa da makusanta a mahaifarsa ta garin Daura.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel