An samu karuwa: Fatima Dangote ta haihu a kasar Amurka

An samu karuwa: Fatima Dangote ta haihu a kasar Amurka

Mun samu labari cewa ‘Diyar babban Mai kudin Najeriya Aliko Dangote watau Fatima Dangote, ta samu karuwa inda ta haifi jaririya. Jaridar The Cable ta rahoto wannan labari 12 ga Agusta, 2019.

Da alamu an yi wannan haihuwa ne a cikin ‘yan kwanakin nan inda labarin ya fara ratsa gari a farkon makon nan. Hakan na zuwa ne kusan bayan shekara guda da rabi da a ka yi aurensu.

Fatima Dangote ta bar Najeriya ne zuwa Amurka a karshen makon da ya wuce. Dangote ta haihu ne a kasar wajen. Sahibin Mijin na ta wani babban Matukin jirgin sama ne wanda ya shahara.

Hajiya Dangote ta na auren Jamilu Abubakar ne wanda Mahaifinsa ya taba riken mukamin babban Sufetan ‘yan sanda a Najeriya. Jamilu shi ne babban Yaron Muhammad D. Abubakar

KU KARANTA: Zaben 2019: ‘Yan gida guda sun fito takarar Gwamna a Jihar Kogi

Fatima da Halima su na cikin ‘Ya ‘yan Dangote. Attajirin ya na matukar Kaunar wadannan ‘Ya ‘ya na sa kamar yadda ya bayyana a ranar auren Fatima da Jamilu wanda ya ce ya dauka tamkar 'Da.

A lokacin da a ka yi auren na su, Mai kudin Duniya, Bill Gates ya samu zuwa, haka kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo da Attajirin nan na Nahiyar Afrika, Mo Ibrahim sun zo.

Manyan ‘yan siyasan gida da su ka halarci bikin da a ka yi a bara sun hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bukola Saraki, Yakubu Dogara. Sarakuna irin su Rilwan Akiolu, sun halarta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel