Babu makawa ambaliyar ruwa za ta mamaye wasu jihohi a Najeriya - NIHSA

Babu makawa ambaliyar ruwa za ta mamaye wasu jihohi a Najeriya - NIHSA

Hukumar kula da harkokin magudanan ruwa ta Najeriya NIHSA (Nigeria Hydrological Services Agency), ta kirayi jihohin kasar nan da su kasance cikin shirin aukuwar ambaliyar ruwa mai yawan gaske a sanadiyar saukar ruwan sama mai tsanani.

Wannan sanarwa ta zo ne cikin wani sako da shugaban hukumar NIHSA na kasa, Injiniya Clement Nze, ya gabatar ga manema labarai cikin birnin Abuja a ranar Laraba.

Babban injiniyan na ruwa ya ce ana sa ran aukuwar ambaliyar mai yawan gaske cikin wasu jihohin kasar nan a sakamakon yadda a yanzu ake ci gaba da shatata ruwan sama tamkar da bakin kwarya.

Injiniya Nze ya ce ambaliyar za ta ci gaba da aukuwa ba kama hannun yaro a watan gobe a sanadiyar cika da batsewar kogin Neja da na Benuwai.

Ya ce akwai yiwuwar jihohi da dama ana Najeriya za su fuskanci musibar ambaliyar ruwa a watanni masu zuwa duba da yadda ruwan sama na mamako ke ci gaba shatata tun bayan da damina ta kama.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta nemi haramtawa Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, wata mata ta haihu a kan itaciyar mangwaro yayin da take neman tsira a daga ambaliyar ruwan data jawo mahaukaciyar guguwa a tsakiyar kasar Mozambique.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel