Wata matar aure ta nemo wa mijinta mata ta biyu yayin da ta dauki juna biyu

Wata matar aure ta nemo wa mijinta mata ta biyu yayin da ta dauki juna biyu

Ko a cikin litattafai da finafinai, ana nuna kishin mutane a kan wanda suke so, musamman a irin zamantake wa ta aure ko soyayya.

Amma duk da hakan sai gashi an samu wata mata a kasar malaysia da ta yi zarra ta hanyar nema wa mijinta mata ta biyu da zata kula da shi yayin da juna biyun da ta dauke da shi ya yi nauyi.

Matar, Khuzatu Atiqh, ta kasance tare da mijinta, Samuel Dzul, tun 2011 kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

A cewar rahoton da jaridar 'Asia One' ta wallafa, Atiqah ta tsinci kan ta cikin yawan laulayi lokacin da take da cikin yaronsu na biyar.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta (Facebook), Atiqah ta bayyana cewa rashin lafiyar ta tayi tsananin da sai a kujera ake tura ta. A cewar ta, "na kasance cikin damuwa a kan halin da miji na da yaran mu zasu shiga idan wani abu ya same ni."

A cikin wannan yanayi ne Atiqah ta yanke sawarar fara nema wa mijinta mata ta biyu, wacce za ta iya kula da shi da 'ya'yansu, kuma a dandalin sada zumunta ne Atiqah ta gano wata mata mai suna Nur Fathonah, wacce daga bisani ta gamsar da mijinta cewa ya kamata ya aure ta a matsayin mata ta biyu.

Atiqh ta sha fama da Fathonah kafin daga bisani ta amince ta zo gidansu domin su karya tare, sannan ta gabatar da ita ga mijinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel