Masu gari: 'Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota

Masu gari: 'Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota

- Diyar Gwamna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Balaraba Ganduje, ta yiwa fitaccen mawakin nan Ado Gwanja wata gagarumar kyauta

- Balaraba ta bai wa mawakin kyautar wata tsaleliyar mota kirar kamfanin Honda Accord baka

- Mawakin ya wallafa hoton motar ne a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa wannan kyauta ta fito daga wajen Balaraba ne

Diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Balaraba Ganduje, ta yiwa fitaccen mawakin matan nan kyautar wata dankareriyar bakar mota kirar Honda Accord.

Ado Gwanja ya wallafa hoton motar a shafinsa na Instagram, inda ya ce; "Alhamdulillahi wannan kyautar ta zo mini daga Balaraba, don ku kara tabbatar da cewa mun bi gidan hallaci, ni ke da uwar gaske madalla da kulawa Hajiya Balaraba," in ji Ado Gwanja.

KU KARANTA: Jerin birane guda 11 da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya

Wannan kyauta dai ba ta zo da mamaki ba, idan zaku tuna Ado Gwanja yana daya daga cikin manyan mawakan jihar ta Kano da suka yi gwamna Ganduje a zaben da aka gabatar a farkon wannan shekarar a jihar ta Kano.

Ko lokacin da aka dinga rade-radin cewa gwamna Ganduje zai sha kasa a lokacin zaben, hakan bai hana mawakin daina wallafa hotunan gwamnan a shafukansa na sada zumunta ba. Hakan ne yasa ake yi masa kallon dan a mutun gwamna Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng