Wasu kayayyaki da sojoji suka kama sun sake tona asirin 'yan kungiyar ISWAP - ONSA

Wasu kayayyaki da sojoji suka kama sun sake tona asirin 'yan kungiyar ISWAP - ONSA

- Sojojin Najeriya da na 159 Troops sun kama wasu manyan motocci dauke da kayayaki na 'yan ta'addan kungiyar ISWAP

- Kayayyakin sun hada da giya cikin robobi, kwayoyi masu saka maye da magungunan kara karfin maza

- Sojojin sun gano haramtattun kayayyakin ne cikin kwallayen taliya da nufin yi wa jami'an tsaro basaja

Ofishin Mai Bawa Shugban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, ONSA ta sanar da cewa sojojin 159 troops sun ragargaza hanyoyin safarar kayayyaki da 'yan kungiyar ta'adda na ISWAP ke amfani da shi.

Mai magana da yawun ONSA, Mista Danjuma Reuben ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin tarayya, Abuja.

Rueben ya ce sojojin sun samu wannan gaggarumin nasarar ne a ranar 23 ga watan Yuli a kan hanyar Gubio zuwa Damasak a cigaba da kokarin kawar da 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Sheikh Ahmad ya fadawa gwamnati yadda za a magance matsalar 'yan shi'a

Ya yi bayanin cewa dakarun sojojin sun kwace wata manyan motocci kirar Hilux biyu dauke da haramtattun kayayaki mallakar 'yan kungiyar ta'addan.

"Da aka bincike motoccin an gano haramtattun kayayaki da suka hada da kayan maye, giya, magungunan kara karfin maza da wasu kayayyakin.

"An boye kayayyakin cikin kwalin taliyar Honey Well domin yi wa jami'an tsaro basaja.

"Direbobin motoccin sun ce an basu umurnin su kai kayayakin kauyen Gudumnali inda ake tunanin daga nan ne za a tafi da kayar wurin shugabanin kungiyar ta ISWAP a Tafkin Chadi.

"Kama wadannan haramtattun kayayyakin musamman kayan kara karfin mazan alama ce da ke nuna irin keta hakkin mata da 'yan kungiyar ta ISWAP ke yi," in shi.

Mai magana da yawun na ONSA ya ce wannan kamun da sojojin su kayi ya tona asirin farfagandar da 'yan kungiyar ke yi na cewa sune musulmi na gaskiya duba da cewa amfani da irin wadannan abubuwan sun saba wa koyarwan addinin musulunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel