El-Zakzaky: Sheikh Ahmad ya fadawa gwamnati yadda za a magance matsalar 'yan shi'a

El-Zakzaky: Sheikh Ahmad ya fadawa gwamnati yadda za a magance matsalar 'yan shi'a

Shugaban kungiyar Ansar-Ud-Deen na kasa, Sheikh Abdulrahman Ahmad a ranar Alhamis ya yi gargadin cewa amfani da karfin bindiga ba zai magance tayar da hankula da 'yan kungiyar Shi'a ke yi a kasar ba.

Ahmad ya ce dole ne gwamnati ta kare sake bullar wata kungiyar 'yan ta'adda da ka iya tasowa idan ba warware rikicin 'yan Shi'a cikin hikima da lalama ba.

A hirar da ya yi da Daily Trust, Malamin addinin Islaman ya ce baya goyon bayan duk wata kungiya da ke yi wa gwamnati bita da kulli amma duk da hakan gwamnati na iya tattaunawa da 'yan kungiyar domin kare afkuwar fitina.

DUBA WANNAN: Adamu Adamu ya fadi aikin da ya yi wa Buhari a baya tun kafin ya nada shi minista

Ya ce alhaki zai rataya kan gwamnati muddin aka cigaba da samun tabarbarewar doka da oda sakamakon cigaba da zanga-zangan da 'Yan Shi'a ke yi tun ranar Litinin a Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa zanga-zangan ta kazanta ne bayan an kashe wani mataimakin kwamishinan 'Yan sanda da dan yi wa kasa hidima da wasu 'yan kungiyar ta IMN wato Shi'a.

A cewar malamin, ya kamata gwamnati ta koyi darasi a kan mutuwar Muhammed Yusuf ba tare da gabatar da shi gaban kotu ba wadda hakan ne ya haifar da Boko Haram.

Shaihin malamin ya ce, "Ya kamata ayi takatsantsan domin kare afkuwar fitina. Doka za tayi aikinta amma tattaunawa shima zai yi amfani. A halin yanzu ma Amurka na tattaunawa da 'Yan Taliban, ba zai yi wu a ce ba za a ayi sulhu da 'yan ta'adda ba a yanzu."

Sheikh Ahmad ya kuma ce ya dace gwamnati ta yi biyaya ga umurnin kotu na bayar da belin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel