Soja marmari daga nesa: Babu wata bindiga da zata iya kashe ni a duniyar nan - Bidiyon wani matsafin soja

Soja marmari daga nesa: Babu wata bindiga da zata iya kashe ni a duniyar nan - Bidiyon wani matsafin soja

- A bayyana bidiyon wani jarumin soja dan kasar Kenya yana harbin kanshi da bindiga, amma taki yi masa illa

- Sojan ya bayyana cewa duk duniya babu wata bindiga da za ta iya yi masa, ciki kuwa harda AK-47 da ake ji da ita a ko ina a duniyar nan

- Sojan dai ya nuna wata riga da yake amfani da ita wacce aka asirce ta da wani bakin asiri

- Mutane dai sun fara maganar irin wadannan sojoji ake bukata a Najeriya, domin kuwa sune daidai da 'yan ta'addar dake addabar kasar

Wani jami'in hukumar soja dan kasar Kenya ya nuna wani asiri da yake dashi bayan ya harbi kanshi da bindiga kuma babu abinda ya same shi.

Sojan dan nahiyar Afirka wanda yake amfani da wata rigar soja wacce aka asirce ta da bakin asiri, ya wallafa wani bidiyo inda yake nuna cewa babu wata bindiga a duniyar nan da za ta iya kashe shi.

KU KARANTA: Tirkashi: Idan kin gama ki san inda dare yayi miki - Abinda wani mutumi ya cewa matarsa kenan bayan ya kamata tana yi masa bincike a waya

Wannan bidiyo da wannan jarumin soja ya wallafa yasa wasu mutanen sun fara maganar cewa irin wadannan sojoji ake bukata a Najeriya, wadanda basu da tsoro, domin kuwa cin zarafin da 'yan ta'addar kasar nan ke yi sai dai a hada su da daidai su.

Har yanzu dai ana ta samun tashe-tashem hankula a wasu kasashe na nahiyar Afirka, wadanda suka hada da Najeriya, Chadi wadanda suke ta fama da matsalar Boko Haram a wasu yankuna na kasashen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel