NDLEA Ta Kama Tsohuwa da Matashiya Dauke da Miyagun Kwayoyi a Filin Jirgin Sama

NDLEA Ta Kama Tsohuwa da Matashiya Dauke da Miyagun Kwayoyi a Filin Jirgin Sama

  • NDLEA ta kama wata ’yar Afirka ta Kudu mai shekara 34 da ake zargi da safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 36.65 a filin jirgin saman Legas
  • Hukumar ta kuma kama wata ’yar Najeriya da ke zaman Amurka mai shekara 62 da aka kama da tabar wiwi mai nauyin kilogram 9.45 da ta shigo dashi daga Amurka
  • Binciken lamarin ya kai ga kama wani dillalin motoci a Legas, yayin da hukumar ta kuma kama wasu mutane tare da kwace miyagun ƙwayoyi a jihohi daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wata ’yar Afirka ta Kudu mai shekara 34, Qhina Beauty, da ake zargi da safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 36.65 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, jihar Legas.

Hukumar ta kuma kama wata ’yar Najeriya da ke zaman Amurka mai shekara 62, Anetor Gloria Ubong, wadda aka samu da tabar wiwi mai nauyin kilogram 9.45 da aka shigo da ita daga Amurka.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi amfani da tafiya kamfen Tinubu, sun tafka mummunan ta'adi a Zamfara

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, hukumar ta ce an kama matan ne a wasu ayyuka daban-daban a filin jirgin saman Legas.

Yadda aka kama masu shigo da kwaya Najeriya
An mamata tsohuwa da ta shigo da kwaya Najreiya | Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Yadda aka kama ’yar Afirka ta Kudu

A cewar NDLEA, jami’anta sun kama Qhina a ranar 7 ga Oktoba, 2026, a sashen tashin jirage na filin jirgin saman Legas, lokacin da take shirin shiga jirgin Qatar Airways zuwa Afirka ta Kudu ta hanyar Doha.

Binciken jakunkunanta guda biyu ya kai ga gano buhunan hodar iblis guda 30 masu nauyin kilogram 36.65. An ce an shirya kayan ne cikin kunshi-kunshi guda bakwai, tare da amfani da barkono busasshe wajen ɓoye su.

Hukumar ta ce Qhina ta bayyana wa jami’an bincike cewa ta zo Najeriya ne a ranar 30 ga Satumba domin karɓo kayan. Ta kuma ce wata ’yar Afirka ta Kudu ce ta ɗauke ta aiki, tare da yi mata alƙawarin biyan rand 20,000 idan ta yi nasarar kai kayan.

An ce ta kuma bayyana sunayen wasu mutane biyu da take zargi suna da alaƙa da lamarin, ciki har da wani da ke Amurka da kuma dillalin motoci a Legas.

Kara karanta wannan

Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 3 har lahira a Arewacin Najeriya

Bayan gudanar da bincike, jami’an NDLEA sun kama dillalin motocin mai shekara 46, Uchenna Victor Umunnakwe, a ranar 14 ga Oktoba a Apple Junction, Ago Palace Way, Legas.

Hukumar ta ce Umunnakwe ya amsa cewa shi ne ya karɓi Qhina a filin jirgin sama tare da kai ta otal-otal kafin lokacin da za ta tashi.

An kama tsohuwa da tabar wiwi

A wani samame daban da aka gudanar a filin jirgin saman Legas ranar 21 ga Oktoba, jami’an NDLEA sun kama Anetor Gloria Ubong, mai shekara 62, wadda ke sana’ar sayar da gidaje a Richmond, Texas, Amurka.

Hukumar ta ce an kama ta ne bayan ta iso Najeriya daga Houston a jirgin United Airlines. Binciken akwatunanta guda biyu ya kai ga gano kunshi-kunshi 18 na tabar wiwi mai nauyin kilogram 9.45.

A cewar hukumar, an ɓoye kayan ne a cikin akwati tare da takardar nannaɗe kyauta.

Ubong ta bayyana cewa ’yarta da wanda zai zama surukinta sun kai mata akwatin a gidanta da ke Amurka domin ta kawo shi Najeriya ga saurayin ’yarta mai suna Jibola.

An kwace miyagun ƙwayoyi a jihohi

Kara karanta wannan

Houthi ta zafafa hare hare kan Saudiyya, ta yi gagarumar barna

Baya ga kama matan biyu, NDLEA ta ce jami’anta sun kama wasu mutane tare da kwace miyagun ƙwayoyi a jihohin Legas, Kano, Bauchi, Neja, Edo, Ondo, Taraba, Oyo da Delta.

A Legas, jami’an hukumar sun kama Eletu Rasheedat mai shekara 41 a yankin Eti-Osa. An ce an samu ƙwayoyin diazepam 5,820, tramadol 780, tabar wiwi mai nauyin kilogram 3.7 da kuma lita 230.25 na wani abin sha da ake kira skuchies.

A jihar Delta kuwa, an kama Peter Ugochukwu mai shekara 51 a Warri, inda aka kwace dubban ƙwayoyin tramadol, kwalaben maganin tari mai ɗauke da codeine da sauran magungunan da ake amfani da su ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, an kama Helen Bakporo Samson mai shekara 46 da tabar wiwi mai nauyin kilogram shida a Warri.

A jihar Kano, samamen da aka kai yankin Gerawa ya kai ga kama Murtala Lawan mai shekara 30 tare da kwace tubalan tabar wiwi 159 masu nauyin kilogram 97.2.

A jihar Taraba, jami’an NDLEA sun kama Raiyanu Misa mai shekara 39 da tubalan tabar wiwi masu nauyin kilogram 60.175 a wurin binciken ababen hawa na Lankaviri da ke ƙaramar hukumar Yorro.

Kara karanta wannan

'Yan ISWAP sun sha wuta, sojojin sama sun soya manyan kwamandojinsu

A jihar Neja kuwa, an kama Emmanuel Ekene mai shekara 26 da ƙwayoyin magunguna 64,000 da suka haɗa da tramadol da diazepam.

NDLEA ta yabawa jami’anta

A Bauchi, jami’an hukumar sun kama Jamilu Mustapha, wanda aka fi sani da Last Card, mai shekara 45, tare da kwace tabar wiwi mai nauyin kilogram 379 a garin Nasaru da ke ƙaramar hukumar Ningi.

Hukumar ta kuma ce jami’anta sun gano tabar wiwi mai nauyin kilogram 583 a wata gona da ke Akure ta Kudu, jihar Ondo. A jihar Edo kuwa, sun lalata gonakin tabar wiwi guda biyu da aka kiyasta za su iya samar da fiye da kilogram 2,000.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ayyukan da suka gudanar, tare da buƙatar su ci gaba da yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng