Najeriya Ta Samu Sauki kan Cutar Ebola bayan Daukar Sabon Mataki

Najeriya Ta Samu Sauki kan Cutar Ebola bayan Daukar Sabon Mataki

  • An dauke mace ɗaya tilo da aka tabbatar ta kamu da Ebola a Najeriya zuwa Switzerland domin samun ƙarin kulawar lafiya
  • Ministan Lafiya, Ali Pate, ya ce yanayin lafiyar matar ya inganta sosai, amma hakan ba yana nufin ta daina iya yaɗa cutar ba
  • NCDC na sa ido kan mutane 53 da suka yi mu’amala da matar, ciki har da 44 da ke da alaƙa da asibitin da aka yi mata magani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Najeriya ta koma ba ta da mara lafiyar Ebola a cikin ƙasar bayan an kwashe mace ɗaya tilo da aka tabbatar ta kamu da cutar.

An tafi da matar ne mai dauke da cutar Ebola zuwa kasar Switzerland domin samun ƙarin kulawar lafiya.

An samu saukin Ebola a Najeriya
Mohammed Ali Pate, ministan lafiya a Najeriya Hoto: Mohammed Ali Pate
Source: Twitter

Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Ali Pate, ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

Ana zargin Ebola ta ci gaba da yaduwa a Najeriya, NCDC ta gano mutane 53 da suka yi mu'amala

Ali Pate ya bayyana cewa an tashi da matar daga Abuja ne da amincewarsa, tare da mijinta, wanda har zuwa lokacin bai nuna alamun kamuwa da cutar ba.

Yanayin lafiyar matar ya inganta

A wani saƙon da ya wallafa, Pate ya ce lafiyar matar ta inganta sosai kafin a dauke ta zuwa Switzerland.

Ya bayyana cewa matar tana cikin kwanciyar hankali, a farke, tana iya magana da sadarwa, yayin da sakamakon gwaje-gwajen lafiyarta ke ƙara komawa kusa da matakan da aka saba gani.

Sai dai ministan ya yi gargaɗin cewa ingantuwar lafiyarta ba lallai ta nuna cewa ta daina iya yaɗa cutar ba.

“Lafiyar mai cutar ta inganta sosai. Tana cikin kwanciyar hankali, a farke, tana magana, kuma sakamakon gwaje-gwajen lafiyarta yana komawa kusa da matakan da aka saba gani. Wannan ba yana nufin ba ta iya yaɗa cutar ba, shi ya sa ake ci gaba da bin tsauraran matakan kariya,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Pate ya yaba wa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da suka kula da matar, tare da jami’an kula da lafiyar jama’a da suka tsara kwashe ta bisa ƙa’idojin da suka dace. Ya ce gwamnati za ta fitar da ƙarin bayani bayan matar da mijinta sun isa inda za su tafi lafiya.

Gwamnati ta ce ana ci gaba da matakan kariya

Ministan ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ana ci gaba da aiwatar da matakan kariya domin shawo kan cutar da aka shigo da ita daga ƙasashen waje.

Ya kuma bukaci jama’a su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, tare da dogaro da sahihan bayanai daga majiyoyin da za a iya amincewa da su.

A cewarsa, ingantuwar lafiyar matar da kwashe ta zuwa ƙasashen waje ba za su sa hukumomi sassauta matakan kariya ba, musamman saboda yiwuwar ci gaba da yaɗuwar cutar.

An dauke mai cutar Ebola
Ministan lafiya, Mohammed Ali Pate Hoto: Mohammed Ali Pate
Source: Twitter

Za tallafawa masu Ebola

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar NCDC ta amince da biyan N100,000 ga kowane mutum da cutar Ebola ta shafa.

An ware kudin ne a matsayin tallafi kowane mako domin tallafa wa waɗanda aka killace ko aka keɓe saboda barkewar cutar Ebola a Abuja R

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng