Masu garkuwa da mutane sun kashe yarinya 'yar shekara 8 a Kano

Masu garkuwa da mutane sun kashe yarinya 'yar shekara 8 a Kano

An gano gawar wata yarinya mai shekaru takwas, Aisha Sani da wata mata ta sace ta makonni biyu da suka gabata a Tudun Wada Quaters da ke birnin Kano.

Aisha tana hanyarta na koma wa gida ne daga makarantar Islamiyya ne tare da 'yan uwan ta yayin da wata mace da ta rufe fuskanta ta sace ta kuma ba ta yi magana da iyayen ta ba na tsawon kwanaki uku.

Bayan mako guda, an aike wa iyayen yarinyar sakon kar ta kwana na tes inda aka sanar da su cewa tana cikin koshin lafiya kuma kada su tayar da hankalin su.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An sake yin gumurzu tsakanin jami'an tsaro da 'Yan Shi'a a Abuja

Amma kwanaki biyu da suka gabata, wadanda su kayi garkuwa da ita sun bukaci a biya su kudin fansa Naira Miliyan 200 kamar yadda wani dan uwan yarinyar da ya nemi a boye sunansa ya fadi.

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci ba bawa mahaifiyar ta kudin fansar domin ta kai musu.

Bayan makonni biyu ana nema, an gano gawar Aisha a ranar Litinin da alamun cewa wadanda su kayi garkuwa da ita sun yi mata rauni.

Iyayen ta sun karbi gawarta domin ayi mata jana'iza bisa tsarin koyarwar addinin musulunci.

Da aka nemi ji ta bakinsu kan lamarin, Rundunar 'Yan sandan jihar sun ce har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin kuma za a gano duk wadanda ke da hannu cikin aikata wannan mummunan aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel