Mace ta nemi kashe ko illata Maigidan ta ya na neman zama ruwan dare a Najeriya

Mace ta nemi kashe ko illata Maigidan ta ya na neman zama ruwan dare a Najeriya

A halin yanzu da a ke ciki, ana yawan samun rikici a gidajen aure inda Mace za ta nemi ta kashe Mijinta ko kuma ta yi masa wani lahani. Masana sun yi magana a game da wannan babbar matsala.

A cikin ‘yan kwanakin nan an yi ta samun wadanda su ka sha da kyar daga hannun Matansu. Daga ciki akwai Aliyu Ibrahim wanda kishin kara aure ya sa Mai dakinsa, Aisha Ali ta watsa masa ruwan zafi a al’aura.

Jaridar Daily Trust ta yi dogon bincike a kan wannan lamari inda ta bankado wasu labaran da ba a san da su ba, tare da gano abubuwan da ke haddasa wadannan matsaloli, da kuma yadda za a bi a kawo karshen su.

Wani babban jami’in Hisbah, Alhaji Wasi’u Muhammad Jinjiri, wanda ya kware wajen sulhun Ma'aurata ya alakanta wannan matsaloli da a ke samu a cikin gidajen aure da tabarbarewar tarbiyya a al’umma.

Muhammad Jinjiri ya nuna cewa babu yarinyar da a ka yi wa tarbiyya nagari da za ta nemi ganin bayan mijinta. Jinjiri ya ce abin da Macen kirki za ta yi, shi ne ta kai kara gaban Iyaye ko kuma gaban hukumar Hisbah.

Shugabar wata kungiya ta manyan Lauyoyin Matan Kano, Huwaila Muhammad Ibrahim, ta daura laifin a kan Iyaye, al’umma, hukuma da su kan su Ma’aurata, inda ta ce kowa bai san matsayi da nauyin da ke gaban sa ba.

Shi kuma Babban Limamin masallacin Al-Furqan da ke Birnin Kano, Dr. Bashir Aliyu ya nuna cewa rashin tarbiyya daga gida da kuma watsi da koyar musulunci da jahilici ne ya jefa ma’urata cikin wannan mummunan hali.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna yayi gargadi a kan maida hankali kan ba jama'a ilmi

Dr. Bashir Aliyu ya ke cewa Masu aure sun yi watsi da tafarkin addini a lamarinsu. A cewarsa dole a samu tasgaro a harkar da a ka manta da Allah da koyarwar Ma’aiki SAW domin kuwa ba za a taba samun wata albarka ba.

Malamin ya ke cewa Matasa da-dama ba su fahimci ainihin abin da aure ya ke nufi ba, wannan ya sa ba a kula da nauyi da hakkin auren. Wata babbar matsalar kuma ita ce a na samun Ma’uratan da ke cin amanar juna a waje.

Wani babban Shehi a fannin dabi’ar Dan Adam a Jami’ar Bayero ta Kano, Aminu Muhammad Fagge, ya bayyana cewa wayewar zamani da tasirin kafofin yada labarai su na cikin abubuwan da su ka haddasa wannan fitina.

Farfesa Aminu Muhammad Fagge ya ke cewa: “Idan ku ka duba, za ku ga cewa yanzu an samu al’adun waje da su ka gurbata zaman auren mu.” "Mutanen waje sun yi tasiri, ga aure ya yi tsada, a na neman juya Mazaje a gida."

Kamar dai yadda Bashir Aliyu ya nuna cewa Fadar Kano za ta kawo kudirin da zai gyara zaman iyali a Majalisa. Wannan Farfesa ya nuna lallai dole gwamnati ta tsoma kan ta cikin wannan matsala domin a samu gyara.

Alhaji Jinjiri na hukumar Hisbah ya nuna cewa akwai bukatar Shari’a ta zama ta na da cewa wajen sha’anin aure. Jinjiri ya ce tun farko a ke bari a na rusa albarkar aure a wasu bukukuwa na fitsara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel