Babban magana: Ana shirin haramta sana’ar adaidaita sahu a Kano

Babban magana: Ana shirin haramta sana’ar adaidaita sahu a Kano

- Hukumar Karota na jihar Kano ta bayyana cewa akwai yiwuwar haramta sana'ar adaidaita sahu a jihar

- Shugaban hukumar, Dr. Baffa Babba Dan’Agundi yace zuwa yanzu ba za su iya yanke hukunci kan lamarin ba amma dai jami'an tsaro na kan gudanar da bincike

- Yace da zaran sun kammala za su tattaro bayanai inda su kuma zasu sake duba domin yanke hukuncin da ya dace

Shugaban hukumar Karota na jihar Kano, Dr. Baffa Babba Dan’Agundi ya bayyana cewa akwai yiwuwar dakatar da ci gaba da sana’ar adaidaita sahu a fadin jihar.

Sai dai kuma Dan’Agundi wanda ya kasance tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, yace zuwa yanzu ba za su iya cewa komai ba a kan sana’ar adaidaitan ba wanda matasan jihar suka yi wa tururuwa wajen gudanarwa.

Ya bayyana cewa Jami’an tsaro na nan suna ci gaba da aiki tare da yin bincike, da zarar sun kammala kuma za su tattaro masu bayanan da aka tace kan lamarin, sannan kuma su sake dubawa domin zartar da hukuncin da ya dace, wanda zai kasance ci gaba da aiwatar da sana’ar ko kuma dakatar da ita kwata-kwata a jihar.

Shugaban kungiyar Karotan ya bayyana hakan ne yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin.

Hon. Dan’Agundi ya ce, da zarar Jami’an tsaro tare da sauran masu daga nan ne za a san abin da ya kamata a yi, amma dai yanzu ba zan yi saurin cewa komai ba, saboda ka da na yi saurin azabarbabi ko riga-Malam-Masallaci.

KU KARANTA KUMA: Ganduje vs Abba: Kotu ta hana Abba Gida-Gida sauyin jerin shaidu

“Hakazalika, kowane irin mataki wannan Hukumar ta karota za ta dauka a kan wannan sana’a ta Adaidaita sahu da kuma sauran abubuwan da hukumar ta ke da hurumi a kai wadanda doka ta sahale mata, sai nan gaba kadan za a ji matsayinta a kai, domin duk abin da zai kawo ci-gaban Kano ta fuskar tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali, shi ne abin da wannan hukumar za ta fi baiwa fifiko ba tare da tsoro ko shakkar wani ba,” in ji Dan'Agundi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel