Tirkashi: Ni dan gidan Dagaci ne, saboda haka babu wanda ya kaini asali a Kano - Ganduje

Tirkashi: Ni dan gidan Dagaci ne, saboda haka babu wanda ya kaini asali a Kano - Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa mutane su kari surutan su babu wanda ya isa ya rushe masarautun jihar Kano

- Ya ce duk cikin mutanen da suke yin surutu a jihar Kano babu wanda ya kai shi asali

- Ya kara da cewa ta gaba da baya shi cikakken Bafulatani ne, saboda haka babu yadda za ayi ya bata al'adun gargajiya

A yau dinnan ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sabbin masarautun jihar Kano guda hudu da ya kirkira suna nan daram-dam babu wanda ya isa ya rushe su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da Sarkin Rano, Mai Martaba Alhaji Tafida Abubakar (Autan Bawo), ya kai masa ziyara tare da tawagar manyan garin da kuma manyan fadarsa.

Ganduje ya fuskanci kalubale kala-kala a lokacin da ya kirkiri sabbin masarautun Bichi, Rano, Karaye da Gaya, inda ya cire su daban daga jikin masarautar Kano. Mutane sun zarge shi a matsayin wanda yake kokarin bata tarihin jihar ta Kano.

KU KARANTA: Allah daya gari ban-ban: Kasar da ake farautar zabiya ana sayar da sassan jikinsu tamkar na dabbobi (Hotuna)

Ya ce: "Na fi su zama Bafulatani, da yawa daga cikinsu basu da wani asali dake da hadi da kabilar Fulani."

Ya kara da cewa: "Wadannan mutanen da suke ganin abinda muka yi bai dace ba babu abinda suka iya sai surutu."

"Babu wanda ya kaini asali da kabilar Fulani, Kakan Kakana na wajen Uba Bafulatani ne. Haka kuma Kakar Kakata ta wajen Uwa ita ma Bafulatana ce," in ji gwamnan.

Ya ce: "Ni dan gidan Dagaci ne. Daga yaya zan kawo hanyar da zata bata wannan muhimmiyar al'ada tamu ta iyaye da kakanni.

"Ina kalubalantar duk wadannan masu surutun banzan su gaya mana wane irin abu suke yi da zai amfani jihar Kano?"

"Ko sunki ko sun so, sabbin masarautu babu wanda ya isa ya rushe su," in ji shi.

"Ina kalubalantar shi (Kwankwaso) ya nuna mana aiki daya da ya kammala wanda ya gada a wajen Malam Ibrahim Shekarau," in ji Gwamna Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel