Allura zata tono garma: Hon. Abdulmumini Jibrin yayi barazanar tona yadda aka yi magudin zaben 2019 a jihar Kano

Allura zata tono garma: Hon. Abdulmumini Jibrin yayi barazanar tona yadda aka yi magudin zaben 2019 a jihar Kano

- Rikicin siyasar jihar Kano dai na kara tsamari, yayin da lamarin ya kai shugabannin jam'iyyar APC din sun fara fadar munanan kalamai ga junansu

- A wannan karon Hon. Abdulmumini Jibrin ne ya bayyana cewa zai tona wani boyayyen asiri da ya faru a jihar ta Kano

- Ya kuma bayyana shugaban jam'iyyar APC na jihar a matsayin dan daba mai tada zaune tsaye

Rikicin babbar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki na kara girmama a jihar Kano tsakanin dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa da kuma manyan yaran Ganduje irinsu Fa'izu Alfindiki, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas da sauran su.

Jibrin ya ce matukar wadannan mutane basu sanyawa bakunansu linzami akan irin bakaken maganganun da suke fada a kansa, to babu makawa zai bayyana wani boyayyen asiri na jihar ta Kano.

KU KARANTA: Kurunkus: Motata ce Adam A. Zango ya zabga muku karyar cewa ya saya miliyan 23 - Zulaihat Ibrahim

Haka kuma dan majalisar ya ragargaji shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas a matsayin mutumin da yake tada zaune tsaye a jihar Kano.

Kofa yayi wannan suka ne a wata hira da yayi da gidan rediyon Kano. Inda ya bayyana shugaban jam'iyyar a matsayin mai amfani da 'yan daba don hana mutane zaman lafiya.

A karshe dan majalisar ya bayyana cewa matukar ba gwamna Ganduje ne ya nemi ayi sulhu ba, ba zai ragawa kowa ba a cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel