Banyankole: Kabilar da uwar amarya ke kwana da ango domin tabbatar da kwazonsa

Banyankole: Kabilar da uwar amarya ke kwana da ango domin tabbatar da kwazonsa

A mafi yawan kabilun nahiyar Afrika, ana dora wa kanwar mahaifiya alhakin fadakar wa da yin nasiha ga budurwar da za a aurar. A mafi yawancin lokuta, kanwar mahaifiya ce ke shirya budurwa domin ta fuskanci kalubalen da ke cikin zaman aure.

Amma lamarin ba haka ya ke ba a kabilar Banyankole da ke kudu maso yammacin kasar Uganda, inda aka dora wa kanwar mahaifiyar budurwar da za a aurar alhakin sanin namijin da za a bawa auren diyar 'yar uwar ta.

Babban aikin kanwar uwar budurwar da za a aurar a kabilar Banyankole shine tabbatar da kuzarin ango ta fuskar saduwa kafin a kai ga aura masa diyar 'yar uwar ta. Domin tabbatar da kuzarin angon, a wasu lokutan, kanwar mahaifiyar kan yi saduwar jima'i da angon diyar 'yar uwarta domin tabbatar da kwazonsa a gado.

Kazalika, kanwar mahaifiyar budurwar za ta bawa angon tabbacin cewa diyarsu cikakkiyar budurwa ce da ba ta taba sanin wani da namiji ba.

Ita ce kuma ke da alhakin tabbatar da cewa diyarsu da zasu aurar ba ta taba sanin wani da namiji ba ta hanyar duba tsiraicinta da yi mata binciken kwakwaf kafin aurar da ita ga saurayin da ke son aurenta.

DUBA WANNAN: Na kwana da kanin mijina ne bisa kuskure, na dauka mijina ne - Matar aure

A wasu lokutan, kanwar mahaifiyar kan kwana tare da ma'auratan a daren farko na aurensu domin ji da ganin yadda zasu ci amarci, saboda kawai ta tabbatar da kuzarin angon da suka aura wa diyarsu.

Duk da ana yi wa wannan al'ada kallon tsohon yayi, ta nuna yadda kabilar Banyankole, musamman masu yaren Bahima, suka bawa rike budurci muhimmanci.

Da zarar diyar 'yan kabilar Bayankole ta cika shekaru 8 a duniya, za a fara saka mata matakai da takunkumi daban-daban domin fara yi mata shirin aure.

Duk da 'yan kabilar Bayankole kan gudanar da al'adu dadan-daban yayin auren 'ya'yansu, al'adar tabbatar da kwazon ango da buducin amarya da kanwar mahaifiyar budurwa ke yi kafin kulla aure ta fi zama babban abun mamaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel