El-Rufai: 'Yan majalisa sun yi daidai da suka ki bawa mai zagina kujerar kwamishina

El-Rufai: 'Yan majalisa sun yi daidai da suka ki bawa mai zagina kujerar kwamishina

- Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yaji dadin hukuncin da majalisar sa ta yanke akan kwamishinan da yake zagin shi a shafin Facebook

- An bayyana cewa Aliyu Jaafar wanda aka so a bai wa mukamin kwamishinan noma na jihar Kaduna ya kalubalanci gwamnatin El-Rufa'i a shekarar 2017

- Gwamnan ya ce a shirye yake ya goyawa duk wani hukunci da majalisar jihar ta yanke baya

Jiya Juma'a ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce 'yan majalisar sa sunyi masa daidai da suka ki tantance kwamishinan da yake zagin shi a shafin Facebook.

A ranar Alhamis dinnan da ta gabata ne, kakakin majalisar jihar Kaduna, Aminu Shagali ya ki bai wa Aliyu Jaafar kujerar kwamishinan noma na jihar Kaduna, bayan an gano cewa ya kalubalanci gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2017.

KU KARANTA: Tirkashi: Amaechi ya fede biri har wutsiya, ya bayyana 'yan siyasar da suka sace kudi suka azurta kansu a kasar nan

Da yake magana lokacin rantsar da kwamishinonin nasa, El-Rufai ya ce: "Muna godiyaga majalisar jihar Kaduna da irin hanyoyin da suka bi wajen tantance kwamishinonin mu. Mun san cewa majalisar taki tantance wani kwamishina guda daya, kuma zamu bayar da kujerar shi ga wani nan ba da dadewa ba.

"Ina ganin abinda suka yi daidai ne, saboda aikinsu ne su dinga duba duk wani abu da muke yi. Kowa tara yake bai cika goma ba. Haka ne yasa hadin guiwar mu da majalisar jihar nan take da matukar amfani. Kuma muna goyon bayan duk wani hukunci da suka yanke," in ji El-Rufai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel