Yan Abuja sun ba gwamnatin tarayya awa 48 ta kawo karshen zanga-zangar yan shi’a

Yan Abuja sun ba gwamnatin tarayya awa 48 ta kawo karshen zanga-zangar yan shi’a

Yan asalin babbar birnin tarayya sun ba gwamnatin tarayya awa 48 don ta kawo karshen yawan zanga-zangar da yan shi’a ke yi a Abuja.

Mutanen yankin sunyi gargadi cewa ci gaba da zanga-zangar a kungiyar ke yi a birnin tarayyar kasarna iya samun cikas daga mutanen Abuja.

Sun bayyana zanga-zangar da kungiyar ke yi a baya-bayan nan amatsayin mai haifar da barazana a yankin sannan sun yi gargadin cewa idan gwamnati ta ki daukar matakan da suka kamata domin yin maganin kungiyar, toh yana iya zama gagarumin matsala.

Da yake Magana da wni sashi da kafar watsa labarai, Kwamad Yunusa Yusuf ya bayyana cewa ya kamata yan Shi’a su shirya kansu a wani wuri, kamar yadda kungiyar “Bring Back Our Girls” ke zanga-zangar ta.

Ya kuma nuna damuwa cewa zanga-zangar yayi sanadiyar raunata mata bakwai yan asalin yankin wadanda a yanzu suke karban magani aa asibitoci daban-daban a fadin birnin.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto abaya cewa Kungiyar yan shi’a sun yi kira ga babban jigon jam’iyyar the All progressives Congress, Bola Tinubu, da ya fada ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar ya saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: An kashe dan Shi'a daya a Kaduna

Mambobin kungiyar na shi’a yayinda suke zanga-zangar ci gaba da tsare El-Zakzaky, sun bayyana cewa a shirye suke da su mutu har sai an saki Shugaban nasu.

Da yake Magana a madadin kungiyar, jagoran kungiyar a kudu maso yamma, Muftau Zakariya, a lokacin zanga-zangar a Lagas, yace kungiyar na da rayuka miliyan 21 da za su bayar a bukatarsu na a saki El-Zakzaky.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel