Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma majalisar dattawa sunayen wasu mutane guda 5 da yake muradin nadawa mukamin kwamishinoni a hukumar sadarwa ta kasa, NCC, inji rahoton jaridar Premiu Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne ciki wata wasika daya aika ma majalisar dake kunshe da sunayen mutanen da kuma mukamansu, inda ya nemi majalisar ta tantance mutanen kafin ya kai ga nadasu, kamar yadda tsarin mulki ya basu dama.

KU KARANTA: Kotu ta daure wata budurwa shekara 11 a Kurkuku saboda cin mutuncin Ganduje

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta wasikar kamar haka; “Bisa bin sashi na 8 (1) na dokokin hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC, ina mika ma majalisar dattawa sunan Injiniya Uba Maska a matsayin kwamishina mai cikakken iko a hukumar NCC.”

Haka zalika shugaban kasa ya nemi sahhalewar majalisar ta amince da mutane uku a matsayin kwamishinonin hukumar NCC, amma wadanda basu da cikakken iko. Sunayen sun hada da Aliyu Abubakar (Arewa maso gabas), Millennia Aboiye (Kudu maso kudu) da Abdulaziz Salman (Arewa ta tsakiya).

A hannu guda kuma, shugaba Buhari ya aika ma majalisar sunan Abu Galadima a matsayin wanda yake so ya nadashi babban daraktan cibiyar horas da manyan jami’an gwamnatin tarayya, NIPPS Kuru, dake jahar Filato.

A wani labarin, majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa da ya haramta hadawa, shigowa, da kuma sayar da fiya fiyan kashe kwari mai suna Sniper a Najeriya, sakamakon ya zama abinda yan Najeriya ke amfani dashi wajen kashe kansu.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuli bayan Sanata Theodore Orji na jahar Abia ya gabatar da kudurin haramta sayar da fiya fiyan saboda yadda ya zama annoba a tsakanin matasan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel